Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Miracles of Christ

193 ayoyi · 30 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yesu ya zazzaga dukan Galili, yana koyarwa a cikin majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin sama, yana kuma warkar da kowace cuta da rashin lafiyar mutane.

  2. Labarinsa ya bazu ko’ina a Suriya, mutane kuwa suka kawo masa dukan waɗanda suke fama da cututtuka iri-iri, da waɗanda suke da zafin ciwo, da masu aljanu, da waɗanda suke masu farfaɗiya, da shanyayyu, ya kuwa warkar da su.

  3. Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin. Ya ce, “Ina so, ka tsabtacce!” Nan da nan aka warkar da shi daga kuturtarsa.

  4. Da Yesu ya zo cikin gidan Bitrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance a gado tana da zazzaɓi.

  5. Ya taɓa hannunta sai zazzaɓin ya sake ta, ta kuwa tashi ta fara yin masa hidima.

  6. Sai ya shiga jirgin ruwa, almajiransa kuwa suka bi shi.

  7. Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci.

  8. Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!”

  9. Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.

  10. Da ya isa ɗayan gefen a yankin Gadarenawa (ko kuwa Gerasenawa), sai ga mutum biyu masu aljanu suna fitowa daga kaburbura suka tarye shi. Su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bin wannan hanya.

  11. Suka yi ihu suka ce, “Me ya haɗa ka da mu, Ɗan Allah?” Ka zo ne nan don ka ji mana kafin lokaci yă yi?

  12. Nesa kaɗan da su kuwa akwai babban garken aladu da yake kiwo.

  13. Aljanun suka roƙi Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.”

  14. Ya ce musu, “Ku tafi!” Sai suka fita suka shiga cikin aladun, dukan garken kuwa ya gangara a guje daga kan tudun zuwa cikin tafkin aladun kuma suka mutu a cikin ruwa.

  15. Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya?’

  16. Amma don ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.”

  17. Mutumin kuwa ya tashi ya tafi gida.

  18. Da taron suka ga haka, sai suka cika da tsoro, suka yabi Allah wanda ya ba wa mutane irin ikon nan.

  19. Da Yesu ya yi gaba daga wurin, sai ya ga wani mutum mai suna Mattiyu zaune a inda ake karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Mattiyu kuwa ya tashi ya bi shi.

  20. Yayinda Yesu yake cin abinci a gidan Mattiyu, masu karɓar haraji da yawa da kuma masu zunubi suka zo suka kuwa ci tare da shi da kuma almajiransa.

  21. Sa’ad da Farisiyawa suka ga haka, sai suka tambayi almajiransa suka ce, “Don me malaminku yake ci tare da masu karɓar haraji, da masu zunubi?”

  22. Da jin wannan, Yesu ya ce, “Ai, ba masu lafiya ba ne su bukatar likita, sai dai marasa lafiya.

  23. Amma ku je ku koyi abin da wannan yake nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba.’Gama ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.”

  24. Yayinda yake faɗin wannan, sai wani mai mulki ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Yanzu-yanzu diyata ta rasu. Amma ka zo ka ɗibiya hannunka a kanta, za tă kuwa rayu.”

  25. A daidai wannan lokaci sai ga wata mace wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini ta raɓo ta bayansa ta taɓa gefen rigarsa.