Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Miracles of Christ: Tempest stilled
Ayoyi game da Tempest stilled
Sai ya shiga jirgin ruwa, almajiransa kuwa suka bi shi.
Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci.
Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!”
Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.
Da suka hau jirgin ruwan, sai iskar ta kwanta.