Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Miracles of Christ: Woman healed of infirmity
Ayoyi game da Woman healed of infirmity
a wurin kuwa, akwai wata mace wadda aljani ya gurgunta, har na shekaru goma sha takwas. Duk ta tanƙware, ba ta ma iya miƙewa ko kaɗan.
Da Yesu ya gan ta, sai ya kirata gaba, ya ce mata, “Mace, an ’yantar da ke daga rashin lafiyarki.”
Sai ya ɗibiya hannuwansa a kanta, nan da nan sai ta miƙe, ta yabi Allah.