Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Quotations and Allusions: Hebrews 8:8, »...I will make a new covenant...«

11 ayoyi · 252 fannoni

Ayoyi game da Hebrews 8:8, »...I will make a new covenant...«

  1. “Lokaci yana zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan yi sabon alkawari da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda.

  2. Ba zai zama kamar alkawarin da na yi da kakanni kakanninsu ba sa’ad da na kama su da hannu na bishe su daga Masar, domin sun take alkawarina, ko da yake na zama miji a gare su,” in ji Ubangiji.

  3. “Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila bayan wannan lokaci,” in ji Ubangiji. “Zan sa dokata a tunaninsu in kuma rubuta ta a zukatansu. Zan zama Allahnsu, za su kuma zama mutanena.

  4. Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabci ba, ko ya koya wa ɗan’uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji,’ domin duk za su san ni, daga ƙaraminsu har zuwa babba,” in ji Ubangiji. “Gama zan gafarta muguntarsu ba zan kuwa ƙara tuna da zunubansu ba.”

  5. Amma Allah ya sami mutane da laifi ya ce, “Ina gaya muku lokaci yana zuwa, sa’ad da zan yi sabon alkawari da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda.

  6. Ba zai zama kamar irin alkawarin da na yi da kakanni-kakanninsu sa’ad da na kama hannunsu don in fitar da su daga Masar ba, domin ba su yi aminci da alkawarina ba, sai na juya musu baya, in ji Ubangiji.

  7. Wannan shi ne alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila, bayan lokacin nan, in ji Ubangiji. Zan sa dokokina a cikin zukatansu, in kuma rubuta su a kan zukatansu. Zan zama Allahnsu, su kuwa za su zama mutanena.

  8. Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa ba, balle mutum yă ce wa ɗan’uwansa, ‘Ka san Ubangiji,’ domin dukansu za su san ni, daga ƙaraminsu zuwa babba.

  9. Gama zan gafarta muguntarsu ba zan kuma ƙara tuna da zunubansu ba.”

  10. “Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su bayan wannan lokaci, in ji Ubangiji. Zan sa dokokina a cikin zukatansu, in kuma rubuta su a kan zukatansu.”

  11. Sai ya ƙara da cewa, “Zunubansu da kurakuransu ba zan ƙara tunawa da su ba.”