Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Quotations and Allusions: Acts 7:32, »I am the God of thy fathers...«

4 ayoyi · 252 fannoni

Ayoyi game da Acts 7:32, »I am the God of thy fathers...«

  1. Sai Allah ya ce, “Ni ne Allah na kakanninka, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub.” Da jin wannan, sai Musa ya ɓoye fuskarsa, domin ya ji tsoro yă dubi Allah.

  2. Game da tashin matattu kuwa, ashe, ba ku karanta a cikin littafin Musa ba, game da labarin ɗan kurmin nan mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, yadda Allah ya yi magana da shi ya ce, ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’?

  3. Sa’ad da ya ga haka, ya yi mamakin abin da ya gani. Da ya yi kusa domin ya duba sosai, sai ya ji muryar Ubangiji ta ce,

  4. ‘Ni ne Allahn kakanninka, Allah na Ibrahim, Ishaku, da kuma Yaƙub.’ Sai Musa ya yi rawan jiki don tsoro, bai kuwa yi karambanin dubawa ba.