Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Quotations and Allusions: Matthew 12:18, »Behold my servant...«

9 ayoyi · 252 fannoni

Ayoyi game da Matthew 12:18, »Behold my servant...«

  1. “Ga bawana, wanda na ɗaukaka, zaɓaɓɓen nan nawa wanda nake jin daɗi; Zan sa Ruhuna a cikinsa zai kuwa kawo adalci ga al’ummai.

  2. Ba zai yi ihu ko ya tā da murya, ko ya daga muryarsa a tituna ba.

  3. Iwan da ta tanƙware ba zai karye ba, ba zai kashe lagwani mai hayaƙi ba. Cikin aminci zai kawo adalci;

  4. ba zai kāsa ko ya karai ba sai ya kafa adalci a duniya. Cikin dokarsa tsibirai za su sa zuciya.”

  5. Wannan kuwa domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya ne cewa,

  6. “Ga bawana da na zaɓa, ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi; zan sa Ruhuna a kansa, zai kuma yi shelar adalci ga al’ummai.

  7. Ba zai yi faɗa ko yă ɗaga murya ba, ba kuwa wanda zai ji muryarsa a kan tituna.

  8. Kyauron da ya tanƙwasa ba zai karye shi ba. Fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba, sai ya jagoranci adalci zuwa ga nasara.

  9. Cikin sunansa al’ummai za su dogara.”