Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Quotations and Allusions: 1 Peter 3:14, »Be not afraid of their terror...«
Ayoyi game da 1 Peter 3:14, »Be not afraid of their terror...«
“Kada ka kira wani abu makirci game da kome da waɗannan mutane suke kira makirci; kada ji tsoron abin da suke tsoro, kada kuma ka firgita game da shi.
Ubangiji Maɗaukaki shi ne za ka ɗauka a matsayi mai tsarki, shi ne wanda za ka ji tsoro, shi ne za ka yi rawar jiki a gabansa,
Amma ko da za ku sha wahala saboda abin da yake daidai, ku masu albarka ne. “Kada ku ji tsoron abin da suke tsoro; kada kuma ku firgita.”
Sai dai a cikin zukatanku ku keɓe Kiristi a matsayin Ubangiji. A kullum, ku kasance a shirye ku ba da amsa ga duk wanda yake neman ku ba da dalilin wannan begen da kuke da shi. Amma ku yi wannan cikin tawali’u da ladabi,