Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Quotations and Allusions: Hebrews 10:16, »This is the covenant that I will make...«

7 ayoyi · 252 fannoni

Ayoyi game da Hebrews 10:16, »This is the covenant that I will make...«

  1. “Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila bayan wannan lokaci,” in ji Ubangiji. “Zan sa dokata a tunaninsu in kuma rubuta ta a zukatansu. Zan zama Allahnsu, za su kuma zama mutanena.

  2. Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabci ba, ko ya koya wa ɗan’uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji,’ domin duk za su san ni, daga ƙaraminsu har zuwa babba,” in ji Ubangiji. “Gama zan gafarta muguntarsu ba zan kuwa ƙara tuna da zunubansu ba.”

  3. Wannan shi ne alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila, bayan lokacin nan, in ji Ubangiji. Zan sa dokokina a cikin zukatansu, in kuma rubuta su a kan zukatansu. Zan zama Allahnsu, su kuwa za su zama mutanena.

  4. Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa ba, balle mutum yă ce wa ɗan’uwansa, ‘Ka san Ubangiji,’ domin dukansu za su san ni, daga ƙaraminsu zuwa babba.

  5. Gama zan gafarta muguntarsu ba zan kuma ƙara tuna da zunubansu ba.”

  6. “Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su bayan wannan lokaci, in ji Ubangiji. Zan sa dokokina a cikin zukatansu, in kuma rubuta su a kan zukatansu.”

  7. Sai ya ƙara da cewa, “Zunubansu da kurakuransu ba zan ƙara tunawa da su ba.”