Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Quotations and Allusions: Romans 11:26, »There shall come out of Zion the Deliverer...«

5 ayoyi · 252 fannoni

Ayoyi game da Romans 11:26, »There shall come out of Zion the Deliverer...«

  1. A ta haka fa, za a yi kafarar laifin Yaƙub, wannan kuma zai zama cikakken amfanin kau da zunubinsa. Sa’ad da ya niƙa duwatsun bagade suka zama kamar allin da aka farfashe kucu-kucu, har ba sauran ginshiƙan Ashera ko bagadan ƙona turare da za a bari a tsaye.

  2. “Mai fansa zai zo Sihiyona, zuwa waɗanda suke cikin Yaƙub da suka tuba daga zunubansu,” in ji Ubangiji.

  3. “Game da ni dai, ga alkawarina da su,” in ji Ubangiji. “Ruhuna, wanda yake a kanka, da kuma maganata da na sa a bakinka ba za tă rabu da bakinka ba, ko daga bakunan ’ya’yanka ba, ko kuwa daga bakunan zuriyarsu ba daga wannan lokaci zuwa gaba da kuma har abada,” in ji Ubangiji.

  4. Ta haka kuwa za a ceci dukan Isra’ila, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mai ceto zai zo daga Sihiyona; zai kawar da rashin bin Allah daga Yaƙub.

  5. Wannan kuwa shi ne alkawarina da su sa’ad da na ɗauke musu zunubansu.”