Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Quotations and Allusions: Romans 10:6, »Who shall ascend into heaven...«

6 ayoyi · 252 fannoni

Ayoyi game da Romans 10:6, »Who shall ascend into heaven...«

  1. Ba ya can sama, balle ku ce, “Wa zai hau sama yă kawo mana, yă kuma furta mana, don mu yi biyayya?”

  2. Ba kuwa yana gaba da teku ba, da za ku ce, “Wa zai haye tekun don yă kawo mana, yă kuma furta mana, don mu yi biyayya?”

  3. A’a, kalmar tana nan dab da ku, tana cikin bakinku da cikin zuciyarku, don ku yi biyayya.

  4. Amma adalcin da yake ga bangaskiya yana cewa, “Kada ka faɗa a zuciyarka, ‘Wa zai hau sama?’ ” (wato, don yă sauko da Kiristi),

  5. “ko kuwa ‘Wa zai gangara can zurfin ƙasa?’ ” (wato, don yă hauro da Kiristi daga matattu).

  6. Amma mene ne aka ce? “Maganar tana kusa da kai; tana cikin bakinka da kuma cikin zuciyarka,” wato, maganar bangaskiyan nan da muke shela.