Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Quotations and Allusions: Matthew 4:6, »He shall give His angels charge...«
Ayoyi game da Matthew 4:6, »He shall give His angels charge...«
Gama zai umarci mala’ikunsa game da kai don su tsare ka a dukan hanyoyinka;
za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.
Ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, yi tsalle ka sauka ƙasa. Gama a rubuce yake, “ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai, za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’”
Gama a rubuce yake, “ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai, su kiyaye ka da kyau;
za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’”