Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Quotations and Allusions: 1 Peter 3:10, »For he that will love life...«

8 ayoyi · 252 fannoni

Ayoyi game da 1 Peter 3:10, »For he that will love life...«

  1. Duk waninku da yake ƙaunar rayuwa yana kuma so yă ga kwanaki masu kyau,

  2. ka kiyaye harshenka daga mugunta da kuma leɓunanku daga faɗar ƙarairayi.

  3. Juyo daga mugunta ku yi alheri; nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.

  4. Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu;

  5. fuskar Ubangiji yana gāba da waɗanda suke aikata mugunta, don yă sa a manta da su a duniya.

  6. Gama, “Duk wanda yake so yă ji daɗin rayuwa, yă kuma ga kwanaki masu kyau dole yă ƙame harshensa daga mugunta leɓunansa kuma daga maganar yaudara.

  7. Dole yă juye daga mugunta, ya aikata nagarta; dole yă nemi salama yă kuma bi ta.

  8. Gama idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kunnuwansa kuma suna jin addu’arsu, amma fuskar Ubangiji tana gāba da masu mugunta.”