Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Quotations and Allusions: Luke 8:10, »...that seeing they might not see...«

7 ayoyi · 252 fannoni

Ayoyi game da Luke 8:10, »...that seeing they might not see...«

  1. Ya ce, “Je ka ka faɗa wa wannan mutane, “ ‘Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba; Kome yawan dubar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.’

  2. A kansu ne aka cika annabcin Ishaya cewa, “ ‘Za ku yi ta ji amma ba za ku taɓa ganewa ba; za ku yi ta kallo amma ba za ku taɓa gani ba.

  3. Saboda, “ ‘ko sun dinga duba, ba za su taɓa gane ba, kuma ko su dinga ji, ba za su taɓa fahimta ba, in ba haka ba, mai yiwuwa, su tuba, a gafarta musu!’ ”

  4. Sai ya ce, “Ku ne aka ba sanin asirin mulkin Allah, amma ga sauran mutane kam, ina magana da misalai, saboda, “ ‘ko da yake suna kallo, ba za su gani ba, ko da yake suna ji, ba za su gane ba.’

  5. “Ya makantar da idanunsu ya kuma taurare zukatansu, don kada su gani da idanunsu, ko su fahimta a zukatansu, ko kuwa su juyo, har in warkar da su.”

  6. Ishaya ya faɗi haka ne, saboda ya hangi ɗaukakar Yesu, ya kuwa yi magana a kansa.

  7. “ ‘Je ka wurin mutanen nan ka ce, “Za ku yi ta ji amma ba za ku fahimta ba; za ku yi ta dubawa, amma ba za ku gani ba.”