Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Quotations and Allusions: Romans 3:10, »There is none righteous, no, not one...«

6 ayoyi · 252 fannoni

Ayoyi game da Romans 3:10, »There is none righteous, no, not one...«

  1. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Wawaye sukan ce a ransu, “Ba Allah.” Sun lalace, ayyukansu kuwa mugaye ne; babu wani da yake yi abu mai kyau.

  2. Ubangiji ya duba daga sama a kan ’yan adam don yă ga ko akwai wani da ya gane, wani wanda yake neman Allah.

  3. Duka sun kauce, duka gaba ɗaya sun zama lalatattu; babu ɗaya wanda yake yin abu mai kyau, ba ko ɗaya.

  4. Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Babu wani mai adalci, babu ko ɗaya;

  5. babu wani mai fahimta, babu wani mai neman Allah.

  6. Duk sun kauce gaba ɗaya, sun zama marasa amfani; babu wani mai aikata nagarta, babu ko ɗaya.”