Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Quotations and Allusions

636 ayoyi · 252 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “muryar mai kira a hamada tana cewa, ‘Ku shirya wa Ubangiji hanya, ku miƙe hanyoyi dominsa.’ ”

  2. Saboda, “ ‘ko sun dinga duba, ba za su taɓa gane ba, kuma ko su dinga ji, ba za su taɓa fahimta ba, in ba haka ba, mai yiwuwa, su tuba, a gafarta musu!’ ”

  3. Ya amsa ya ce, “Daidai ne Ishaya ya yi annabci game da ku munafukai; kamar yadda yake a rubuce cewa, “ ‘Waɗannan mutane da baki suke girmama ni, amma zukatansu sun yi nesa da ni.

  4. A banza suke mini sujada, koyarwarsu, dokokin mutane ne kawai.’

  5. Gama Musa ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’kuma, ‘Duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.’

  6. Where their worm dieth not, and the fire is not quenched.

  7. Amma a farkon halitta, Allah ya ‘halicce su miji da mace.’

  8. ‘Saboda wannan dalili, mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa,

  9. su biyun kuma za su zama jiki ɗaya.’Saboda haka, su ba mutum biyu ba ne, amma mutum ɗaya.

  10. Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, kada ka cuci wani, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’”

  11. Waɗanda suka yi gaba, da kuma waɗanda suke biye, duk suka ɗaga murya, suna cewa, “Hosanna!” “Mai albarka ne wanda yake zuwa a cikin sunan Ubangiji!”

  12. Da yake koya musu, sai ya ce, “Ashe, ba a rubuce yake ba cewa, ‘Za a kira gidana, gidan addu’a na dukan al’ummai ba’?Amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’”

  13. Ba ku taɓa karanta wannan Nassi ba, “ ‘Dutsen da magina suka ƙi, shi ne kuwa ya zama dutsen kusurwan gini.

  14. Suka ce, “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, in ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata babu ’ya’ya, dole mutumin ya auri gwauruwar, yă kuma samo wa ɗan’uwansa ’ya’ya.

  15. Game da tashin matattu kuwa, ashe, ba ku karanta a cikin littafin Musa ba, game da labarin ɗan kurmin nan mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, yadda Allah ya yi magana da shi ya ce, ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’?

  16. Yesu ya ce, “Wadda ta fi girma duka, ita ce wannan. ‘Ku saurara, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne.

  17. Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.’

  18. Na biyun ita ce, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’Ba wata doka da ta fi waɗannan.”

  19. Dawuda da kansa ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana sai na sa abokan gābanka a ƙarƙashin sawunka.” ’

  20. Yesu ya ce musu, “Dukanku za ku ja da baya ku bar ni, gama yana a rubuce cewa, “ ‘Zan bugi makiyayin tumaki, tumakin kuwa za su warwatse.’

  21. And the scripture was fulfilled, which saith, And he was numbered with the transgressors.

  22. A daidai sa’a ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”).

  23. Zai sha gaban Ubangiji, a ruhu da kuma iko irin na Iliya, domin yă juye zukatan iyaye ga ’ya’yansu, marasa biyayya kuma ga zama masu biyayya don yă kintsa mutane su zama shiryayyu domin Ubangiji.”

  24. (yadda yake a rubuce a Dokar Ubangiji cewa, “Kowane ɗan fari, za a keɓe shi ga Ubangiji”),

  25. don kuma su miƙa hadaya bisa ga abin da aka faɗa a Dokar Ubangiji cewa, “kurciyoyi biyu ko ’yan tattabarai biyu.”