Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Quotations and Allusions

636 ayoyi · 252 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. don ka buɗe idanun makafi ka ’yantar da kamammu daga kurkuku kuma kunce ɗaurarrun kurkuku masu zama cikin duhu.

  2. Da kaina na rantse, bakina ya furta cikin dukan mutunci kalmar da ba za a janye ba. A gabana kowace gwiwa za tă durƙusa; ta wurina kowane harshe zai rantse.

  3. ya ce, “Ɗan ƙaramin abu ne ka zama bawana don ka maido da kabilar Yaƙub ka kuma dawo da waɗannan na Isra’ilawan da na kiyaye. Zan kuma mai da kai haske ga Al’ummai, don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.”

  4. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “A lokacin tagomashina zan amsa muku, kuma a ranar ceto zan taimake ku; zan kiyaye ku zan kuma sa ku zama alkawari ga mutane, don ku maido da ƙasa ku kuma sāke raba gādon kufai,

  5. “Yanzu kuma me nake da shi a nan?” In ji Ubangiji. “Gama an kwashe mutanena ba a bakin kome ba kuma waɗanda suka mallake su sun yi musu ba’a, Kullum ana cin gaba da yin wa sunana saɓo.

  6. Me ya fi wannan kyau a kan duwatsu a ga ƙafafu na masu kawo labari mai daɗi waɗanda suke shelar salama, waɗanda suke kawo labari mai daɗi, waɗanda suke shelar ceto, waɗanda suke ce wa Sihiyona, “Allahnki yana mulki!”

  7. Ku fita, ku fita daga can! Kada ku taɓa wani abu marar tsarki! Ku fita daga cikinta ku zama da tsarki, ku da kuke ɗaukan kayan aikin Ubangiji.

  8. Amma ba za ku fita a gaggauce ba ko ku tafi da gudu; gama Ubangiji zai ja gabanku, Allah na Isra’ila zai kasance mai tsaron bayanku.

  9. haka zai ba al’ummai masu yawa mamaki, sarakuna kuma za su riƙe bakunansu don mamaki. Gama abin da ba a faɗa musu ba, shi za su gani, kuma abin da ba su ji ba, shi za su fahimta.

  10. Wa ya gaskata saƙonmu kuma ga wa hannun Ubangiji ya bayyana?

  11. Tabbatacce ya ɗauki cututtukanmu ya kuma daure da baƙin cikinmu duk da haka muka ɗauka Allah ya hukunta shi ne, ya buge shi ya kuma sa ya sha azaba.

  12. Amma aka yi masa rauni saboda laifofinmu, aka ƙuje shi saboda kurakuranmu; hukuncin da ya kawo mana salama ya kasance a kansa, kuma ta wurin mikinsa ya sa muka warke.

  13. Aka wulaƙanta shi aka kuma yi masa azaba, duk da haka bai buɗe bakinsa ba; aka kai shi kamar ɗan rago zuwa wurin yanka, kuma kamar tunkiya a gaban masu askinta tana shiru, haka bai buɗe bakinsa ba.

  14. Da wulaƙanci da kuma hukunci aka ɗauke shi aka tafi. Wa kuwa zai yi maganar zuriyarsa? Gama an kawar da shi daga ƙasar masu rai; saboda laifin mutanena aka kashe shi.

  15. Aka yi jana’izarsa tare da mugaye, aka binne shi tare da masu arziki, ko da yake bai taɓa yin wani tashin hankali ba, ko a sami ƙarya a bakinsa.

  16. Saboda haka zan ba shi rabo tare da manya, zai kuma raba ganima tare da masu ƙarfi, domin ya ba da ransa har mutuwa, aka kuma lissafta shi tare da masu laifofi. Gama ya ɗauki zunubin mutane masu yawa, ya kuma yi roƙo saboda laifofinsu.

  17. “Ki rera, ya ke bakararriya, ke da ba ki taɓa haihuwa ba; ki ɓarke da waƙa, ki yi sowa don farin ciki, ke da ba ki taɓa naƙuda ba; domin ’ya’yan mace mai kaɗaici sun fi na mai miji yawa,” in ji Ubangiji.

  18. Ubangiji zai koya wa dukan ’ya’yanki maza, da girma kuma salamar ’ya’yanki zai zama.

  19. Ku kasa kunne ku kuma zo gare ni; ku saurare ni, don ranku ya rayu. Zan yi madawwamin alkawari da ku, zan nuna muku ƙaunata marar ƙarewa da na yi wa Dawuda alkawari.

  20. waɗannan ne zan kai tsattsarkan dutsena in sa su yi farin ciki a gidana na addu’a. Hadayunsu na ƙonawa da sadakokinsu za su zama abin karɓa a bagadena; gama za a ce da gidana gidan addu’a domin dukan al’ummai.”

  21. Ƙafafunsu sukan gaggauta zuwa aikata zunubi; suna da saurin zub da jini. Tunaninsu mugaye ne; lalaci da hallaka sun shata hanyoyinsu.

  22. Ba su san hanyar salama ba; babu adalci a hanyoyinsu. Sun mai da su karkatattun hanyoyi; babu wanda zai yi tafiya a kansu ya sami salama.

  23. “Mai fansa zai zo Sihiyona, zuwa waɗanda suke cikin Yaƙub da suka tuba daga zunubansu,” in ji Ubangiji.

  24. “Game da ni dai, ga alkawarina da su,” in ji Ubangiji. “Ruhuna, wanda yake a kanka, da kuma maganata da na sa a bakinka ba za tă rabu da bakinka ba, ko daga bakunan ’ya’yanka ba, ko kuwa daga bakunan zuriyarsu ba daga wannan lokaci zuwa gaba da kuma har abada,” in ji Ubangiji.

  25. Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina, domin Ubangiji ya shafe ni domin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta. Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci, don in yi shelar ’yanci don ɗaurarru in kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu