Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Quotations and Allusions

636 ayoyi · 252 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. gama himma da nake yi wa gidanka yana ƙunata, kuma zagi na masu zaginka yana fāɗuwa a kaina.

  2. Bari teburin da aka shirya a gabansu yă zama musu tarko; bari yă zama sakamakon laifi da kuma tarko.

  3. Bari idanunsu yă dushe don kada su gani, bayansu kuma yă tanƙware har abada.

  4. Bari wurinsu yă zama kufai; kada ka bar wani yă zauna a tentunansu.

  5. Zan buɗe bakina da misalai, zan faɗi ɓoyayyun abubuwa, abubuwan dā,

  6. ya sauko da Manna wa mutanensa don su ci, ya ba su hatsin sama.

  7. “Na ce, ‘Ku “alloli” ne; dukanku ’ya’yan Mafi Ɗaukaka’ ne.

  8. Na sami Dawuda bawana; da mai na mai tsarki na shafe shi.

  9. Gama zai umarci mala’ikunsa game da kai don su tsare ka a dukan hanyoyinka;

  10. za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.

  11. Ubangiji ya san tunanin mutum; ya san cewa tunaninsu banza ne.

  12. gama shi ne Allahnmu mu mutanen makiyayansa ne, garke kuwa a ƙarƙashin kulawarsa. Yau, in kuka ji muryarsa,

  13. “Kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a Meriba, kamar yadda kuka yi a wancan rana a Massa a hamada,

  14. inda kakanninku suka gwada suka kuma jarraba ni, ko da yake sun ga abin da na yi.

  15. Shekara arba’in na yi fushi da wancan tsara; na ce, ‘Su mutane ne waɗanda zukatansu suka kauce, kuma ba su san hanyoyina ba.’

  16. Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”

  17. Dukan waɗanda suke bauta wa siffofi sun sha kunya, waɗanda suke fariya da gumaka, ku yi masa sujada, dukanku alloli!

  18. A farkon fari ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne.

  19. Za su hallaka, amma za ka ci gaba; duk za su tsufe kamar riga. Kamar riga za ka canja su za a kuwa zubar da su.

  20. Amma kana nan yadda kake, kuma shekarunka ba za su taɓa ƙarewa ba.

  21. Ya mai da iska suka zama ’yan saƙonsa harsunan wuta kuma bayinsa.

  22. Da kalmomin ƙiyayya sun kewaye ni; sun tasar mini ba dalili.

  23. Bari kwanakinsa su zama kaɗan; bari wani yă ɗauki wurinsa na shugabanci.

  24. Ta Dawuda. Zabura ce. Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.”

  25. Ubangiji ya rantse ba zai kuma canja zuciyarsa ba, “Kai firist ne har abada, bisa ga tsarin Melkizedek.”