Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Quotations and Allusions

636 ayoyi · 252 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yanzu kukan Isra’ilawa ya kai gare ni, na kuma ga yadda Masarawa suke wulaƙanta su

  2. To, fa, sai ka tafi. Ina aikan ka wurin Fir’auna don ka fitar da mutanena Isra’ilawa daga Masar.”

  3. Amma na bar ka ka rayu domin in nuna maka ikona, domin kuma sunana yă zama abin darajantawa a dukan duniya.

  4. “Dole a ci shi a cikin gida ɗaya; kada a kai naman waje. Kada a karya wani daga ƙasusuwansa.

  5. “Keɓe mini kowane ɗan fari. Ɗan fari wanda ya fara buɗe mahaifa a cikin Isra’ilawa nawa ne, ko na mutum ko na dabba.”

  6. sai ku miƙa kowane ɗan fari ga Ubangiji. Duk ɗan farin dabbobinku na Ubangiji ne.

  7. Da suka gwada a mudu, wanda ya tattara da yawa bai sami mafi yawa ba, wanda kuma ya tattara kaɗan bai sami ƙanƙani ba. Kowane mutum ya tattara daidai bukatarsa.

  8. za ku zama firistoci masu tsarki da kuma al’umma keɓaɓɓiya a gare ni.’ Waɗannan su ne kalmomin da za ka faɗa wa Isra’ilawa.”

  9. Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai hukunta duk wanda ya mai da sunansa banza.

  10. Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki.

  11. Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

  12. Ba za ka yi kisankai ba.

  13. Ba za ka yi zina ba.

  14. Ba za ka yi sata ba.

  15. Ba za ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka ba.

  16. Ba za ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko duk abin da yake na maƙwabcinka ba.”

  17. “Duk wanda ya la’anta mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi.

  18. ido don ido, haƙori don haƙori, hannu don hannu, ƙafa don ƙafa,

  19. “Kada ku yi maganar saɓo ga Allah, ko ku la’anta mai mulkin mutanenku.

  20. Musa ya kuma ɗauki jinin, ya yayyafa a kan mutanen ya ce, “Wannan shi ne jinin alkawarin da Ubangiji ya yi da ku, bisa ga dukan waɗannan kalmomi.”

  21. Sai ka lura ka yi su daidai bisa ga fasalin da aka nuna maka a kan dutse.

  22. Sa’ad da mutane suka ga Musa ya daɗe bai sauko daga dutse ba, sai suka taru kewaye da Haruna suka ce, “Zo, ka yi mana alloli waɗanda za su yi mana jagora. Game da wannan Musa wanda ya fitar da mu daga Masar dai, ba mu san abin da ya faru da shi ba.”

  23. Haruna ya amsa musu ya ce, “Ku tuttuɓe zoban zinariya waɗanda suke kunnuwan matanku, da na ’ya’yanku maza da mata, ku kawo mini.”

  24. Saboda haka dukan mutane suka tuttuɓe ’yan kunnensu suka kawo wa Haruna.

  25. Sai ya karɓi abubuwan da suka ba shi, ya yi gunki na siffar ɗan maraƙi, ya sassaƙa shi da kayan aiki. Sa’ad da mutane suka gani, sai suka tā da murya suka ce, “Waɗannan su ne allolinku, ya Isra’ila, waɗanda suka fitar da ku daga Masar.”