Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prayer

720 ayoyi · 120 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ta haka ba za mu juye mu bar ka ba; ka rayar da mu, za mu kuwa kira bisa sunanka.

  2. Cikin damuwarku kun yi kira na kuwa kuɓutar da ku, na amsa muku daga girgijen tsawa; na gwada ku a ruwan Meriba. Sela

  3. Ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya fitar da ku daga Masar. Ku buɗe bakinku zan kuwa cika shi.

  4. Waƙa ce. Zabura ta Asaf. Ya Allah, kada ka yi shiru; kada ka tsaya cik, ya Allah, kada ka daina motsi.

  5. Dubi yadda abokan gābanka suke fariya, dubi yadda maƙiyanka suke ɗaga kansu.

  6. Ka mai da su kamar ɗan tsiron da kan karye, iska ta yi ta turawa, ya Allahna, kamar yayin da iska take hurawa,

  7. kamar yadda wuta ke cin kurmi ko harshen wutar da take ci a kan duwatsu,

  8. haka za ka kore su da iska mai ƙarfi ka kuma firgita su da guguwarka.

  9. Ka rushe fuskokinsu da kunya don mutane su nemi sunanka, ya Ubangiji.

  10. Bari su kasance cikin kunya da taƙaici; bari su hallaka cikin wulaƙanci.

  11. Bari su san cewa kai, wanda sunansa ne Ubangiji, cewa kai kaɗai ne Mafi Ɗaukaka a bisa dukan duniya.

  12. Addu’ar Dawuda. Ka ji, ya Ubangiji, ka kuma amsa mini, gama ni matalauci ne mai bukata kuma.

  13. Ka tsare raina, gama na ba da kaina gare ka. Kai ne Allahna; ka ceci bawanka wanda ya dogara gare ka.

  14. Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, gama na yi kira gare ka dukan yini.

  15. Ka ba bawanka farin ciki gama gare ka, ya Ubangiji, na miƙa raina.

  16. Kai mai gafartawa da kuma mai alheri ne, ya Ubangiji, cike da ƙauna ga dukan waɗanda suke kira gare ka.

  17. Ka ji addu’ata, ya Ubangiji; ka saurari kukata na neman jinƙai.

  18. A lokacin wahala zan yi kira gare ka, gama za ka amsa mini.

  19. Ka ba ni alamar alherinka, don abokan gābana su gani su kuma sha kunya, gama kai, ya Ubangiji, ka taimake ni ka kuma ta’azantar da ni.

  20. Waƙa ce, Zabura ta ’ya’yan Kora maza. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga mahalat leyannotmaskil na Heman dangin Ezra. Ya Ubangiji, Allah wanda ya cece ni, dare da rana ina kuka a gabanka.

  21. Bari addu’ata ta zo a gabanka; ka kasa kunne ga kukata.

  22. idanuna ba sa gani sosai saboda baƙin ciki. Ina kira gare ka, ya Ubangiji, kowace rana; na tā da hannuwana zuwa gare ka.

  23. Amma ina kuka gare ka neman taimako, ya Ubangiji; da safe addu’ata kan zo gabanka.

  24. Don me, ya Ubangiji, ka ƙi ni ka kuma ɓoye fuskarka daga gare ni?

  25. Ya Ubangiji, ina ƙaunar mai girma ta dā, wadda cikin amincinka ka rantse wa Dawuda?