Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prayer: Praying daily in the morning
Ayoyi game da Praying daily in the morning
Da safe, ya Ubangiji, ka ji muryata; da safe na gabatar da bukatuna a gabanka in kuma jira da sa zuciya.
Amma ina kuka gare ka neman taimako, ya Ubangiji; da safe addu’ata kan zo gabanka.
Bari safiya ta kawo mini maganar ƙaunarka marar ƙarewa, gama na sa zuciyata a gare ka. Ka nuna mini hanyar da zan bi, gama a gare ka na miƙa raina.
Ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai; muna marmarinka. Ka zama ƙarfinmu kowace safiya, cetonmu a lokacin damuwa.