Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prayer: With desire to be answered
Ayoyi game da With desire to be answered
Ka ji muryata sa’ad da na yi kira, ya Ubangiji; ka yi mini jinƙai ka kuma amsa mini.
Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni sa’ad da nake cikin damuwa. Ka juye kunnenka gare ni; sa’ad da na yi kira, ka amsa mini da sauri.
Ka cece mu ka kuma taimake mu da hannunka na dama, domin waɗanda kake ƙauna su kuɓuta.
Zabura ta Dawuda. Ya Ubangiji, ka ji addu’ata, ka saurari kukata don neman jinƙai; cikin amincinka da adalcinka ka amsa mini.