Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prayer

720 ayoyi · 120 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ku tafi daga gare ni, dukanku masu aikata mugunta, gama Ubangiji ya ji kukata.

  2. Ubangiji ya ji kukata saboda jinƙansa; Ubangiji ya karɓi addu’ata.

  3. Dukan abokan gābana za su sha kunya su kuma karaya; za su juya da kunya nan da nan.

  4. Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai, gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.

  5. Gama shi da yakan ɗauki fansa a kan mai kisa yakan tuna; ba ya ƙyale kukan masu wahala.

  6. Ka tashi, ya Ubangiji, kada ka bar wani yă yi nasara; bari a hukunta al’ummai a gabanka.

  7. Ka buge su da rawar jiki, ya Ubangiji; bari al’ummai su sani su mutane ne kurum. Sela

  8. Cikin fariyarsa mugun mutum yakan cuci marasa ƙarfi, waɗanda yake kama cikin makircin da ya shirya.

  9. Ka karye hannun mugaye da kuma mugun mutum; ka nemi hakki daga gare shi saboda muguntar da ba za a gane ba.

  10. Kakan ji, ya Ubangiji sha’awar mai shan wahala; kakan ƙarfafa su, ka kuma saurari kukansu,

  11. Addu’a ce ta Dawuda. Ka ji, ya Ubangiji, roƙona na adalci; ka saurari kukata. Ka kasa kunne ga addu’ata, ba ta fitowa daga leɓuna masu ƙarya.

  12. Na kira gare ka, ya Allah, gama za ka amsa mini; ka kasa kunne ka kuma ji addu’ata.

  13. Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo, na kuwa kuɓuta daga abokan gābana.

  14. Cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji; Na yi kuka ga Allahna don taimako. A Haikalinsa ya ji muryata, Kukana na neman taimako ya kai kunnensa.

  15. Ka biya masa bukatar zuciyarsa ba ka kuwa hana masa roƙon da ya yi da leɓunansa ba. Sela

  16. Ya nemi ka ba shi rai, ka kuwa ba shi, tsawo kwanaki, har abada abadin

  17. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da salon “Matar Zomon Safiya.” Zabura ta Dawuda. Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni? Me ya sa ka yi nisa da cetona, ka yi nesa daga kalmomin nishina?

  18. Ya Allahna, na yi kuka da rana, amma ba ka amsa ba, da dare kuma ban yi shiru ba.

  19. A gare ka ne kakanninmu suka sa bege; sun dogara ka kuwa cece su.

  20. Sun yi kuka gare ka suka kuma sami ceto; a gare ka suka dogara kuma ba su sha kunya ba.

  21. Amma kai, ya Ubangiji, kada ka yi nisa; Ya Ƙarfina zo da sauri don ka taimake ni.

  22. Gama bai rena ko yă ƙyale wahalar masu shan wuya ba; bai ɓoye fuskarsa daga gare shi ba amma ya saurari kukansa na neman taimako.

  23. Ta Dawuda. A gare ka Ya Ubangiji, na miƙa raina.

  24. Ba wanda yake sa bege a gare ka da zai taɓa shan kunya, amma za su sha kunya su da suke tayarwa babu dalili.

  25. Ka tuna, ya Ubangiji da jinƙai da kuma ƙaunarka mai girma, gama suna nan tun dā.