Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prayer

720 ayoyi · 120 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “An daɗe yana ƙi, amma a ƙarshe ya ce cikin tunaninsa, ‘Ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane ba,

  2. amma don gwauruwan nan ta dame ni, zan tabbatar cewa ta sami adalci, domin kada tă gajiyar da ni, da yawan zuwanta.’ ”

  3. Sai Ubangiji ya ce, “Ku ji fa abin da alƙalin nan, marar gaskiya, ya ce.

  4. Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke masa kuka, dare da rana adalci ba? Zai ci gaba da ƙin sauraronsu ne?

  5. Ina gaya muku, zai tabbatar sun sami adalci, ban da ɓatan lokaci. Amma sa’ad da Ɗan Mutum ya dawo, zai sami bangaskiya a duniya ke nan?”

  6. Ku yi tsaro kullum, ku yi addu’a don ku iya kuɓuta daga dukan waɗannan abubuwa da suke kusan faruwa, don ku iya tsayawa a gaban Ɗan Mutum.”

  7. Sai ya ɗauki burodi ya yi godiya, ya kakkarya ya ba su, da cewa, “Wannan jikina ne, da aka bayar dominku. Ku riƙa yin haka don tunawa da ni.”

  8. Sai ya janye daga wurinsu, misalin nisan jifa, ya durƙusa a ƙasa ya yi addu’a,

  9. “Uba, in ka yarda, ka ɗauke mini wannan kwaf, amma ba nufina ba, sai dai naka.”

  10. Domin tsananin azaba, sai ya ƙara himma cikin addu’a, zuffansa kuma na ɗigowa ƙasa kamar jini.

  11. Sai ya ce, “Yesu, ka tuna da ni sa’ad da ka shiga mulkinka.”

  12. Yesu ya amsa, ya ce masa, “Gaskiya nake faɗa maka, yau ɗin nan, za ka kasance tare da ni, a mulkina a sama.”

  13. Yesu ya amsa mata ya ce, “Da kin san kyautar Allah, da kuma wanda yake roƙonki ruwan sha, da kin roƙe shi, shi kuwa da ya ba ki ruwan rai.”

  14. Ku Samariyawa ba ku san abin da kuke yi wa sujada ba; mu kuwa mun san abin da muke yi wa sujada, gama ceto daga Yahudawa yake.

  15. Duk da haka, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya yi, da masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a Ruhu da kuma gaskiya, gama irin waɗannan masu sujada ne Uba yake nema.

  16. Allah ruhu ne, masu yi masa sujada kuwa dole su yi masa sujada a ruhu, da gaskiya kuma.”

  17. Sa’an nan Yesu ya ɗauki burodin, ya yi godiya, ya kuma rarraba wa waɗanda suke zaune gwargwadon abin da ya ishe su. Haka kuma ya yi da kifin.

  18. Sai ga waɗansu jiragen ruwa daga Tibariya suka iso kusa da wurin da mutanen suka ci burodi bayan Ubangiji ya yi godiya.

  19. Mun san cewa Allah ba ya sauraron masu zunubi. Yakan saurari mai tsoronsa mai aikata nufinsa.

  20. Kuma zan yi duk abin da kuka roƙa cikin sunana, don Ɗan ya kawo ɗaukaka ga Uban.

  21. Za ku iya roƙe ni kome a cikin sunana, zan kuwa yi.

  22. In kun kasance a cikina kalmomina kuma suka kasance a cikinku, ku roƙi kome da kuke so, za a kuwa ba ku.

  23. Ba ku kuka zaɓe ni ba, a’a, ni ne na zaɓe ku na kuma naɗa ku ku je ku ba da ’ya’ya-’ya’yan da za su dawwama. Uba kuwa zai ba ku duk abin da kuka roƙa cikin sunana.

  24. A ranan nan, ba za ku sāke tambaya ta kome ba. Gaskiya nake gaya muku, Ubana zai ba ku kome da kuka roƙa cikin sunana.

  25. Har yanzu dai ba ku roƙi kome cikin sunana ba. Ku roƙa za ku kuwa samu, farin cikinku kuwa zai zama cikakke.