Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prayer

720 ayoyi · 120 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. To, da Daniyel ya ji labarin cewa an fitar da doka, sai ya tafi gidansa a ɗakinsa na sama inda tagogin ɗakin suke duban wajen Urushalima. Sau uku yakan durƙusa yă yi addu’a yana yin godiya ga Allahnsa, kamar yadda ya saba yi.

  2. Sai na juya wurin Ubangiji Allah na roƙe shi ta wurin addu’a da koke-koke, cikin azumi, ina saye da tsummoki, na kuma zauna a cikin toka.

  3. Na yi addu’a ga Ubangiji Allahna na furta laifina. “Ya Ubangiji, mai alfarma da kuma Allah mai banrazana, wanda yake cika alkawarinsa na ƙauna ga duk wanda ya ƙaunace shi ya kuma kiyaye dokokinsa,

  4. mun yi zunubi muka kuma yi ba daidai ba. Mu mugaye ne da kuma ’yan tawaye; mun juya wa umarninka da shari’unka baya.

  5. Ba mu saurari bayinka annabawa ba, waɗanda suka yi magana a sunanka ga sarakunanmu da masu mulkinmu da iyayenmu, da kuma dukan mutanen ƙasa.

  6. “Ubangiji, kai mai adalci ne, amma a yau kunya ta rufe mu, mutanen Yahuda da mutanen Urushalima da na dukan Isra’ila, waɗanda suke kusa da kuma nesa, a dukan ƙasashen da ka warwatsa mu saboda rashin amincinmu a gare ka.

  7. Ya Ubangiji, mu da sarakunanmu, da masu mulkinmu da iyayenmu kunya ta rufe mu saboda mun yi maka zunubi.

  8. Ubangiji Allahnmu mai jinƙai ne, mai gafartawa ne kuma, ko da yake mun yi masa tawaye;

  9. ba mu yi biyayya ga Ubangiji Allahnmu ba, ba mu kuma kiyaye shari’unsa da ya ba mu ta wuri bayinsa annabawa ba.

  10. Dukan Isra’ila sun karya dokokinka suka kuma juya maka baya, sun ƙi yi maka biyayya. “Saboda haka la’anoni da rantsuwar hukunce-hukuncen da suke a rubuce a cikin Dokar Musa, bawan Allah, sun kama mu domin mun yi maka zunubi.

  11. Ka cika kalmomin da ka yi a kanmu da kuma a kan masu mulkinmu ta wurin kawo mana babban bala’i. A duniya duka ba a taɓa yin wani abu kamar yadda aka yi wa Urushalima ba.

  12. Kamar yadda yake a rubuce cikin Dokar Musa, dukan wannan bala’i ya sauko a kanmu, duk da haka ba mu nemi tagomashin Ubangiji Allahnmu ta wurin barin aikatawa zunubanmu, mu kuma mai da hankali a kan gaskiyarka ba.

  13. Ubangiji bai yi wata-wata wajen kawo mana bala’i ba, domin Ubangiji Allahnmu mai adalci ne a cikin dukan abin da yake yi; duk da haka ba mu yi masa biyayya ba.

  14. “Yanzu, ya Ubangiji Allahnmu, wanda ya fito da mutanensa daga Masar ta hannu mai ƙarfi wanda kuma ya yi wa kansa sunan da ya dawwama har yă zuwa yau, mun yi zunubi, mun yi abin da ba daidai ba.

  15. Ya Ubangiji, ta wurin kiyaye dukan ayyukanka na adalci, ka huce daga fushinka da hukuncinka da ka yi a kan Urushalima, birninka, tudunka mai tsarki. Zunubinmu da laifofin iyayenmu sun mai da Urushalima da kuma mutanenka abin ba’a ga dukan waɗanda suke kewaye da mu.

  16. “Yanzu, ya Allahnmu, ka ji addu’o’i da koke-koken bayinka. Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka duba da rahama wurinka mai tsarki da ya zama kango.

  17. Ka kasa kunne, ya Allah, ka kuma ji; ka buɗe idanunka ka kuma ga yadda birninka ya zama kango, birnin da yake ɗauke da Sunanka. Ba cewa muna roƙonka saboda mu masu adalci ba ne, amma saboda girman jinƙanka.

  18. Ya Ubangiji, ka saurara! Ya Ubangiji ka gafarta! Ya Ubangiji, ka ji ka kuma yi wani abu! Saboda sunanka, ya Allahna, kada ka yi jinkiri, domin da sunanka ake kiran birninka da jama’arka.”

  19. Ya yi kokawa da mala’ika ya kuma rinjaye shi; ya yi kuka ya kuma yi roƙo don tagomashi. Ya same shi a Betel ya kuma yi magana da shi a can,

  20. Bari firistocin da suke yin hidima a gaban Ubangiji, su yi kuka tsakanin filin haikali da bagade. Bari su ce, “Ka cece mutanenka, ya Ubangiji. Kada ka bar gādonka yă zama abin dariya, da abin ba’a a cikin al’ummai. Me zai sa a ce a cikin mutane, ‘Ina Allahnsu yake?’ ”

  21. Ta haka Ubangiji zai yi kishin ƙasarsa yă kuma ji tausayin mutanensa.

  22. Ubangiji zai amsa musu ya ce, “Ina aika da hatsi, sabon ruwan inabi, da mai, isashe da zai ƙosar da ku sosai; ba kuma zan ƙara maishe ku abin dariya ga al’ummai ba.

  23. Amma dukan waɗanda suka nemi Ubangiji za su tsira. Kamar yadda Ubangiji ya ce, gama a Dutsen Sihiyona da Urushalima akwai ceto, a cikin waɗannan da Ubangiji ya kira.

  24. Ga abin da Ubangiji ya ce wa gidan Isra’ila. “Ku neme ni ku rayu;

  25. kada ku nemi Betel, kada ku je Gilgal, kada ku yi tafiya zuwa Beyersheba. Gama ba shakka Gilgal za tă tafi bauta, za a kuwa mai da Betel ba kome ba.”