Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Praise

490 ayoyi · 106 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ka aiko da haskenka da gaskiyarka, bari su bishe ni bari su kawo ni ga dutsenka mai tsarki, zuwa wurin da kake zama.

  2. Sa’an nan zan tafi bagaden Allah, ga Allah, farin cikina da murnata. Zan yabe ka da garaya, Ya Allah, Allahna.

  3. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ku tafa hannuwanku, dukanku al’ummai; ku yi sowa ga Allah da muryoyin farin ciki.

  4. Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai; ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai.

  5. Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya; ku rera zabura ta yabo gare shi.

  6. Waƙa ce. Zabura ta ’ya’yan Kora maza. Ubangiji mai girma ne, kuma mafificin yabo, a birnin Allahnmu, dutsensa mai tsarki.

  7. Shi wanda ya miƙa hadayun godiya yakan girmama ni, ya kuma shirya hanya saboda in nuna masa ceton Allah.”

  8. Ya Ubangiji, ka buɗe leɓunana, bakina kuwa zai furta yabonka.

  9. Zan yabe ka har abada game da abin da ka yi; a cikin sunanka zan dogara, gama sunanka yana da kyau. Zan yabe ka a gaban tsarkakanka.

  10. Ga Allah, wanda nake yabon maganarsa, ga Ubangiji, wanda nake yabon maganarsa,

  11. Ina ƙarƙashin alkawari gare ka, ya Allah; zan miƙa hadayuna na godiya gare ka.

  12. Zuciyata tana nan daram, ya Allah, zuciyata tana nan daram; zan rera in kuma yi kaɗe-kaɗe.

  13. Ka farka, raina! Ku farka, garaya da molo! Zan sa safe yă farka.

  14. Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai; zan rera game da kai a cikin mutane.

  15. Ya ƙarfina, na rera yabo gare ka; kai, ya Allah, kai ne kagarata, Allah mai ƙaunata.

  16. Sa’an nan zan riƙa rera yabo ga sunanka in kuma cika alkawarina kowace rana.

  17. Domin ƙaunarka ta fi rai kyau, leɓunana za su ɗaukaka ka.

  18. Zan yabe ka muddin raina, kuma a cikin sunanka zai ɗaga hannuwana.

  19. Raina zai ƙoshi kamar da abinci mafi kyau; da leɓunan rerawa bakina zai yabe ka.

  20. A gadona na tuna da kai; ina tunaninka dukan dare.

  21. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Wata waƙa. Yabo ya dace da kai, ya Allah, a Sihiyona; a gare ka za mu cika alkawuranmu

  22. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Waƙa. Zabura. Ku yi sowa ta farin ciki ga Allah, dukan duniya!

  23. Ku rera ɗaukaka ga sunansa; ku sa yabonsa yă zama da ɗaukaka!

  24. Dukan duniya sun rusuna a gabanka suna rera yabo gare ka, suna rera yabo ga sunanka.” Sela

  25. Ku yabi Allahnku, ya mutane, bari a ji ƙarar yabonsa;