Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Praise: All creation

11 ayoyi · 106 fannoni

Ayoyi game da All creation

  1. Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji daga sammai, yabe shi a bisa sammai.

  2. Yabe shi, dukanku mala’ikunsa, yabe shi, dukanku rundunarsa na sama.

  3. Yabe shi, rana da wata, yabe shi, dukanku taurari masu haskakawa.

  4. Yabe shi, ku bisa sammai da kuma ku ruwan bisa sarari.

  5. Bari su yabi sunan Ubangiji, gama ya umarta aka kuwa halicce su.

  6. Ya sa su a wurarensu har abada abadin; ya ba da umarnin da ba zai taɓa shuɗe ba.

  7. Yabi Ubangiji daga duniya, ku manyan halittun teku da kuma dukan zurfafan teku,

  8. walƙiya da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da gizagizai, hadirin iskar da suke biyayya da umarnansa,

  9. ku duwatsu da dukan tuddai, itatuwa masu ’ya’ya da dukan al’ul,

  10. namun jeji da dukan dabbobin gida, ƙanana halittu da tsuntsaye masu firiya,

  11. Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji.