Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Praise: His mercy

32 ayoyi · 106 fannoni

Ayoyi game da His mercy

Tace bisa littafi
  1. Bayan suka yi shawara tare da shugabanni, sai ya zaɓi mutanen da za su ja gaban sojoji suna waƙa ga Ubangiji suna yabonsa saboda tsarkinsa suna cewa, “Ku yi godiya ga Ubangiji, gama ƙaunarsa dawwammamiya ce har abada.”

  2. Maskil na Etan dangin Ezra. Zan rera game da ƙauna mai girma ta Ubangiji har abada; da bakina zan sanar da amincinka a dukan zamanai.

  3. Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.

  4. Bari Isra’ila yă ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”

  5. Bari gidan Haruna yă ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”

  6. Bari waɗanda suke tsoron Ubangiji su ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”

  7. Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi. Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  8. Ku yi godiya ga Allahn alloli. Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  9. Ku yi godiya ga Ubangijin iyayengiji. Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  10. Gare shi wanda shi kaɗai yake aikata abubuwan banmamaki, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  11. Wanda ta wurin ganewarsa ya yi sammai, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  12. Wanda ya shimfiɗa duniya a kan ruwaye, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  13. Wanda ya yi manyan haskoki, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  14. Rana don tă yi mulkin yini, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  15. Wata da taurari kuma don su yi mulkin dare; Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  16. Gare shi wanda ya kashe ’ya’yan fari Masar Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  17. Ya kuma fitar da Isra’ila daga cikinsu Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  18. Da hannu mai ƙarfi da hannu mai iko; Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  19. Gare shi wanda ya raba Jan Teku biyu Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  20. Ya kawo Isra’ila ta tsakiyarsa, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  21. Amma ya share Fir’auna da mayaƙansa cikin Jan Teku; Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  22. Gare shi wanda ya bi da mutanensa cikin hamada, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  23. Wanda ya buge manyan sarakuna, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  24. Ya karkashe manyan sarakuna, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  25. Sihon sarkin Amoriyawa Ƙaunarsa madawwamiya ce.