Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Praise: With the whole heart
Ayoyi game da With the whole heart
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ga muryar “Mutuwar Ɗa.” Zabura ta Dawuda. Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata; zan faɗa dukan abubuwan banmamakinka.
Yabi Ubangiji. Zan ɗaukaka Ubangiji da dukan zuciyata a cikin majalisar masu aikata gaskiya da kuma a cikin taro.
Ta Dawuda. Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata; a gaban “alloli” zan rera yabo.