Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Praise: Deliverance
Ayoyi game da Deliverance
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. Na jira da haƙuri ga Ubangiji; ya juya wurina ya kuma ji kukata.
Ya ɗaga ni daga rami marar fāɗi, daga laka da taɓo; ya sa ƙafafuna a kan dutse ya kuma ba ni tsayayyen wuri don in tsaya.
Ya sa sabuwar waƙa a bakina, waƙar yabo ga Allahna. Da yawa za su gani su tsorata su kuma dogara ga Ubangiji.
Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda bai bari aka yayyage mu da haƙoransu ba.