Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Praise

490 ayoyi · 106 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Bari mutane su yabe ka, ya Allah; bari dukan mutane su yabe ka.

  2. Bari al’ummai su yi murna su kuma rera don farin ciki, gama kana mulkin mutanenka da adalci kana kuma bi da al’umman duniya. Sela

  3. Rera wa Allah, rera yabo ga sunansa, ku ɗaukaka wanda yake hawa a kan gizagizai; sunansa Ubangiji ne, ku kuma yi farin ciki a gabansa.

  4. Yabo ya tabbata ga Ubangiji, ga Allah Mai Cetonmu, wanda kullum yake ɗaukan nauyinmu. Sela

  5. Ku yabi Allah cikin taro mai girma; yabi Ubangiji cikin taron Isra’ila.

  6. Ku rera wa Allah, ya masarautan duniya, ku rera yabo ga Ubangiji, Sela

  7. gare shi wanda yake hawan daɗaɗɗen sararin sama, wanda yake tsawa da babbar murya.

  8. Ku yi shelar ikon Allah, wanda ɗaukakarsa take a bisa Isra’ila, wanda ikonsa yake a cikin sarari.

  9. Zan yabe sunan Allah cikin waƙa in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya.

  10. Bari sama da ƙasa su yabe shi, tekuna da dukan abin da yake motsi a cikinsu,

  11. Amma bari dukan masu nemanka su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka; bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce, “Bari Allah yă sami ɗaukaka!”

  12. Daga haihuwa na dogara gare ka; kai ka kawo ni daga cikin mahaifiyata. Kullayaumi zan yabe ka.

  13. Na zama kamar abin sa zuciya ga yawanci, amma kai ne katangata mai ƙarfi.

  14. Bakina ya cika da yabonka, ina furta darajarka dukan yini.

  15. Amma game da ni, kullayaumi zan kasance da sa zuciya; zan yabe ka sau da sau.

  16. Bakina zai ba da labarin adalcinka, zai yi maganar cetonka dukan yini, ko da yake ban san yawansa ba.

  17. Zan yabe ka da garaya saboda amincinka, ya Allah; zan rera yabo gare ka da molo, Ya Mai Tsarki na Isra’ila.

  18. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Mai muryar “Kada A Hallaka.” Zabura ta Asaf. Waƙa ce. Muna maka godiya, ya Allah, muna maka godiya, gama Sunanka yana kusa; mutane na faɗin ayyukanka masu banmamaki.

  19. Sa’an nan mu mutanenka, tumakin makiyayarka, za mu yabe ka har abada; daga tsara zuwa tsara za mu yi ta ba da labarin yabonka.

  20. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit. Ta Asaf. Ku rera don farin ciki ga Allah ƙarfinmu; ku yi sowa ga Allah na Yaƙub!

  21. Masu albarka ne waɗanda suke zama a gidanka; kullum suna ta yabonka. Sela

  22. Zan yabe ka, ya Ubangiji Allahna, da dukan zuciyata; zan ɗaukaka sunanka har abada.

  23. Maskil na Etan dangin Ezra. Zan rera game da ƙauna mai girma ta Ubangiji har abada; da bakina zan sanar da amincinka a dukan zamanai.

  24. Sammai na yabon abubuwan banmamakinka, ya Ubangiji, amincinka shi ma, a cikin taron tsarkakanka.

  25. Yabo ya tabbata ga Ubangiji har abada!