Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Praise

490 ayoyi · 106 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Bari yabon Allah yă kasance a bakunansu takobi mai kaifi kuma a hannuwansu,

  2. don su ɗau fansa a kan al’ummai da kuma hukunci a kan mutane,

  3. don su ɗaura sarakuna da sarƙoƙi, manyan garinsu da sarƙoƙin ƙarfe,

  4. don su yi hukuncin da aka rubuta a kansu. Wannan ne ɗaukakar dukan tsarkakansa. Yabi Ubangiji.

  5. Yabi Ubangiji. Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki; yabe shi a cikin sammai na ikonsa.

  6. Yabe shi saboda ayyukansa masu iko; yabe shi saboda mafificin girmansa.

  7. Yabe shi da ƙarar kakaki, yabe shi da garaya da molo,

  8. yabe shi da ganga kuna taka rawa, yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa,

  9. yabe shi da kuge mai ƙara, yabe shi da kuge masu ƙara sosai.

  10. Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji.

  11. Suna kiran juna, “Mai Tsarki, Mai Tsarki, Mai Tsarki! Ubangiji Maɗaukaki ne; duniya ta cika da ɗaukakarsa.”

  12. A wannan rana za ku ce, “Zan yabe ka, ya Ubangiji. Ko da yake a dā ka yi fushi da ni, amma yanzu ka daina fushi da ni ka kuwa ta’azantar da ni.

  13. Tabbatacce Allah shi ne mai cetona; zan dogara gare shi ba kuwa zan ji tsoro ba. Ubangiji, Ubangiji, ne ƙarfina da waƙata; ya zama mai cetona.”

  14. Da farin ciki zan ɗebo ruwa daga rijiyoyin ceto.

  15. A wannan rana za ku ce, “Yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa; a sanar da wannan abin da ya aikata a cikin al’ummai, a kuma yi shela cewa sunansa mai girma ne.

  16. Ku rera ga Ubangiji, gama ya aikata manyan abubuwa; bari a sanar da wannan ga dukan duniya.

  17. Ku tā da murya ku kuma rera don farin ciki, ya ku mutanen Sihiyona, gama Mai Tsarki na Isra’ila da girma yake a cikinku.”

  18. Sun daga muryoyinsu, sun yi sowa ta farin ciki; daga yamma sun furta darajar Ubangiji.

  19. Saboda haka a gabas sun ɗaukaka Ubangiji, a ɗaukaka sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila, a cikin tsibiran teku.

  20. Daga iyakokin duniya mun ji waƙoƙi, “Ɗaukaka ga Mai Adalcin nan.” Amma na ce, “Na lalace, na lalace! Kaitona! Munafukai sun ci amana! Da munafunci munafukai sun ci amana!”

  21. Ya Ubangiji, kai ne Allahna; zan ɗaukaka ka in kuma yabi sunanka, gama cikin cikakken aminci ka yi abubuwa masu banmamaki, abubuwan da aka shirya tun da.

  22. kuma fansassu na Ubangiji za su komo. Za su shiga Sihiyona da rerawa; matuƙar farin ciki zai mamaye su. Murna da farin ciki za su sha kansu, baƙin ciki kuma da nishi za su gudu.

  23. Gama kabari ba zai yabe ka ba, matattu ba za su rera yabonka ba; waɗanda suka gangara zuwa rami ba za su sa zuciya ga amincinka ba.

  24. Masu rai, masu rai, su suke yabonka, kamar yadda nake yi a yau; iyaye za su faɗa wa ’ya’yansu game da amincinka.

  25. Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji, ku yi yabonsa daga iyakar duniya, ku da kuka gangara zuwa teku, da kome da yake cikinsa, ku tsibirai, da waɗanda suke zama a cikinsu.