Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Praise

490 ayoyi · 106 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Bakina zai yi magana cikin yabon Ubangiji. Bari kowace halitta ta yabi sunansa mai tsarki har abada abadin.

  2. Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji, ya raina.

  3. Zan yabi Ubangiji dukan kwanakina; zan rera yabo ga Allahna muddin raina.

  4. Kada ka sa zuciyarka ga sarakuna, ga mutane masu mutuwa, waɗanda ba sa iya ceto.

  5. Sa’ad da numfashinsu ya rabu da su sai su koma ƙasa; a wannan rana shirye-shiryensu sun zama banza.

  6. Mai albarka ne wanda Allah na Yaƙub ne taimakonsa, wanda sa zuciyarsa yana a kan Ubangiji Allahnsa.

  7. Mahaliccin sama da ƙasa, teku, da kome da yake cikinsu, Ubangiji, wanda yake mai aminci har abada.

  8. Yakan biya bukatun mutanen da aka danne ya kuma ba da abinci ga mayunwata. Ubangiji yakan ’yantar da ’yan kurkuku,

  9. Ubangiji yakan ba wa makafi ido, Ubangiji yakan ɗaga waɗanda aka rusunar da su ƙasa, Ubangiji yana ƙaunar masu adalci.

  10. Ubangiji yana tsaron baƙi yana kuma lura da marayu da kuma gwauruwa, amma yakan lalatar da hanyoyin mugaye.

  11. Ubangiji yana mulki har abada, Allahnki, ya Sihiyona, daga zamani zuwa zamani. Yabi Ubangiji.

  12. Yabi Ubangiji. Yana da kyau a rera yabai ga Allahnmu, abu mai daɗi ne daidai ne kuma a yabe shi!

  13. Ubangiji ya gina Urushalima; ya tattara kamammu na Isra’ilan da aka kai bauta.

  14. Ya warkar da masu raunanar zuciya ya ɗaɗɗaura miyakunsu.

  15. Ya lissafta yawan taurari ya kuma kira kowannensu da suna.

  16. Shugabanmu mai girma ne mai iko duka; ganewarsa ba shi da iyaka.

  17. Ubangiji yana kula da masu sauƙinkai yakan yar da mugaye a ƙasa.

  18. Rera wa Ubangiji waƙar godiya; ku kada garaya ga Allahnmu.

  19. Ya rufe sararin sama da gizagizai; yana tanada wa duniya ruwan sama yana kuma sa ciyawa tă yi girma a kan tuddai.

  20. Yakan tanada wa shanu abinci da kuma saboda ’ya’yan hankaki sa’ad da suka yi kira.

  21. Jin daɗinsa ba ya a ƙarfin doki, balle farin cikinsa yă kasance a ƙafafun mutum;

  22. Ubangiji yakan yi farin ciki a waɗanda suke tsoronsa, waɗanda suke sa zuciya a ƙaunarsa marar ƙarewa.

  23. Ki ɗaukaka Ubangiji, ya Urushalima; ki yabi Allahnki, ya Sihiyona.

  24. Gama yana ƙarfafa ƙyamaren ƙofofinki yana kuma albarkace mutanenki a cikinki.

  25. Yana ba da salama ga iyakokinki yana kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau.