Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Praise

490 ayoyi · 106 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Bari su rera game da hanyoyin Ubangiji, gama ɗaukakar Ubangiji da girma take.

  2. Tabbatacce masu adalci za su yabi sunanka masu aikata gaskiya kuma za su zauna a gabanka.

  3. Ta Dawuda. Yabo ya tabbata ga Ubangiji dutsena, wanda ya horar da hannuwana don yaƙi, yatsotsina don faɗa.

  4. Shi ne Allah mai ƙaunata da kuma kagarata, katangata da mai cetona, garkuwata, wanda nake neman mafaka daga gare shi, wanda ya sa mutane a ƙarƙashina.

  5. Zan rera sabuwar waƙa gare ka, ya Allah; a kan molo mai tsirkiya goma zan yi maka kiɗi,

  6. Zabura ce ta yabo. Ta Dawuda. Zan ɗaukaka ka, ya Allahna, Sarki; zan yabi sunanka har abada abadin.

  7. Kowace rana zan yabe ka in kuma ɗaukaka sunanka har abada abadin.

  8. Ubangiji da girma yake ya kuma cancanci yabo girmansa ya fi ƙarfin ganewar mutum.

  9. Tsara guda za tă yi maganar ayyukanka ga wata tsara; za su yi magana game da manyan ayyukanka.

  10. Za su yi zancen ɗaukakarka mai daraja, zan kuma yi tunani a kan ayyukanka masu banmamaki.

  11. Za su yi magana game da ikon ayyukanka masu bantsoro, zan kuma yi shelar manyan ayyukanka.

  12. Za su yi bikin yalwar alherinka suka kuma rera adalcinka da farin ciki.

  13. Ubangiji mai alheri da kuma tausayi, mai jinkirin fushi cike kuma da ƙauna.

  14. Ubangiji nagari ne ga duka; yana tausayin dukan abubuwan da ya yi.

  15. Dukan abubuwan da ka yi za su yabe ka, ya Ubangiji; tsarkakanka za su ɗaukaka ka.

  16. Za su yi maganar ɗaukakar mulkinka za su kuma yi zancen ikonka,

  17. saboda dukan mutane su san manyan ayyukanka da ɗaukakar darajar mulkinka.

  18. Mulkinka madawwamin mulki ne, sarautarka kuma za tă dawwama cikin dukan zamanai. Ubangiji mai aminci ne ga dukan alkawuransa mai ƙauna kuma ga dukan abubuwan da ya yi.

  19. Ubangiji yana riƙe da dukan waɗanda suka faɗi yana kuma ɗaga dukan waɗanda aka rusunar da su ƙasa.

  20. Idanun kowa yana dogara gare ka, kana kuma ba su abincinsu a lokacin da ya dace.

  21. Ka buɗe hannunka ka kuma ƙosar da sha’awar kowane abu mai rai.

  22. Ubangiji mai adalci ne cikin dukan hanyoyinsa yana kuma nuna ƙauna ga dukan abubuwan da ya yi.

  23. Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi, ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya.

  24. Yakan cika sha’awar waɗanda suke tsoronsa; yakan ji kukansu yă kuma cece su.

  25. Ubangiji yakan lura da dukan waɗanda suke ƙaunarsa, amma dukan mugaye zai hallaka su.