Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Titles and Names of Christ

138 ayoyi · 117 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ka tashi, ka tashi! Ka yafa wa kanka ƙarfi, Ya hannun Ubangiji; ka farka, kamar a kwanakin da suka wuce, kamar a zamanai na dā. Ba kai ba ne wanda ya yayyanka Rahab gunduwa-gunduwa, wanda ya soki dodon ruwan nan?

  2. Duba, bawana zai aikata abubuwa da hikima; za a tā da shi a kuma ɗaga shi da ɗaukaka ƙwarai.

  3. Wa ya gaskata saƙonmu kuma ga wa hannun Ubangiji ya bayyana?

  4. Duba, na mai da shi shaida ga mutane, shugaba da kuma jagorar mutane.

  5. “Mai fansa zai zo Sihiyona, zuwa waɗanda suke cikin Yaƙub da suka tuba daga zunubansu,” in ji Ubangiji.

  6. Za ki sha madarar al’ummai a kuma shayar da ke da nonon sarauta. Sa’an nan za ki san cewa ni, Ubangiji, ni ne Mai Cetonki, Mai Fansarki, Mai Ikon nan na Yaƙub.

  7. Cikin dukan damuwarsu shi ma ya damu, mala’ikan da yake gabansa ya cece su. Cikin ƙauna da jinƙai ya fanshe su; ya kuma ɗaga su ya riƙe su dukan kwanakin dā

  8. “Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan tā da wa Dawuda Reshen adalci, Sarki wanda zai yi mulki da hikima ya kuma yi abin da yake gaskiya da kuma daidai a ƙasar.

  9. A cikin zamaninsa za a ceci Yahuda Isra’ila kuma zai zauna lafiya. Sunan da za a kira shi ke nan, Ubangiji Adalcinmu.

  10. A maimakon haka, za su bauta wa Ubangiji Allahnsu Dawuda sarkinsu kuwa, wanda na tayar musu.

  11. Zan sa musu makiyaya guda, bawana Dawuda, zai kuwa lura da su; zai kula da su ya kuma zama makiyayinsu.

  12. Zan tanada musu ƙasar da aka sani don hatsinta, ba za su kuma ƙara zama abin da yunwa za tă fara musu a ƙasa ba ko su sha zargin sauran al’ummai.

  13. “Sai ka sani ka kuma fahimci wannan; Tun daga sa’ad da aka kafa doka don a maido a kuma sāke gina Urushalima har sai Shafaffen nan, mai mulki, ya zo, za a yi shekara arba’in da tara, da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu. Za a sāke gina ta a yi mata tituna da mafaka.

  14. Ki tattara sojojinki, ya ke birnin mayaƙa, gama an kewaye mu da yaƙi. Za su bugi kumatun mai mulkin Isra’ila da sandar ƙarfe.

  15. “Amma ke, Betlehem ta Efrata, ko da yake ke ƙarama ce daga cikin zuriyarki a Yahuda, daga cikinki wani zai zo domina wanda zai yi mulkin Isra’ila, wanda asalinsa tun fil azal ne.”

  16. Zan girgiza dukan al’ummai, marmarin kowace al’umma kuma zai taso, sa’an nan zan cika gidan nan da ɗaukaka,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  17. “ ‘Ka saurara, ya babban firist Yoshuwa, kai da abokanka da suke zaune a gabanka, ku da kuke alamun abubuwan da za su zo. Zan kawo bawana, wanda yake Reshe.

  18. Ka ce masa ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ga mutumin da sunansa ne Reshe, zai kuma ratse daga inda yake yă gina haikalin Ubangiji.

  19. Ki yi murna ƙwarai, ya Diyar Urushalima! Ki yi sowa, Diyar Urushalima! Duba, ga sarkinki yana zuwa wurinki, mai adalci yana kuma da ceto, mai tawali’u yana kuma hawan jaki, yana a kan ɗan aholaki, a kan ’yar jaka.

  20. “Tashi, ya takobi, gāba da makiyayina, mutumin da yake kusa da ni sosai!” In ji Ubangiji Maɗaukaki. “Kashe makiyayin, sai tumakin su watse, in kuma tayar wa ƙananan.

  21. “Duba, zan aika manzona, wanda zai shirya hanya a gabana. Sa’an nan a farat ɗaya Ubangiji wanda kuke nema zai zo haikalinsa. Manzon alkawari, wanda kuke sa zuciya kuwa zai zo,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  22. Amma ku da kuke girmama sunana, ranar adalci za tă fito tare da warkarwa a fikafikanta. Za ku kuwa fita kuna tsalle kamar ’yan maruƙan da aka sake daga garke.

  23. Za tă haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.”

  24. “Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel” (wanda yake nufin “Allah tare da mu”).

  25. suka yi tambaya suka ce, “Ina shi wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Gama mun ga tauraronsa a gabas mun kuwa zo ne domin mu yi masa sujada.”