Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Scriptures

159 ayoyi · 108 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Wannan shi ne abin da muke sanarwa, ba da kalmomin da muka koya ta wurin hikimar mutum ba, amma da kalmomin da Ruhu yake koyarwa, muna faɗin gaskiya ta ruhaniya da kalmomin ruhaniya.

  2. Mutumin da ba shi da Ruhu, ba ya yarda da abubuwan da suka fita daga Ruhun Allah, domin wauta ce a gare shi. Ba kuwa zai fahimce su ba, domin ta Ruhu ne ake fahimtarsu.

  3. Waɗannnan abubuwa sun same su ne, domin su zama abubuwan koyi, aka kuma rubuta su domin a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana.

  4. Gama abu farko mafi muhimmancin da na karɓo shi ne na ba ku cewa Kiristi ya mutu domin zunubanmu bisa ga Nassi,

  5. Ba ma tallar maganar Allah don riba yadda waɗansu mutane da yawa suke yi. A maimakon haka, muna magana cikin Kiristi a gaban Allah da gaskiya, kamar mutanen da aka aika daga Allah.

  6. Shi ya sa muka gwaninta a matsayinmu na masu hidimar sabon alkawari ba ta rubutacciyar Dokar ba, amma ta Ruhu; don Dokar, kisa take yi, Ruhu kuwa yana ba da rai.

  7. Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafuncin da suke abubuwan kunya. Ba ruwanmu da ruɗu, ko yin ƙarya da kalmar Allah. Sai dai muna faɗin gaskiya a fili. Ta haka ne kowa zai yi shaidar gaskiyarmu a gaban Allah cikin zuciyarsa.

  8. Dukan waɗanda suka dogara ga kiyaye Doka la’anannu ne, gama a rubuce yake cewa, “La’ananne ne duk wanda bai ci gaba da yi dukan abubuwan da aka rubuta a Littafin Doka ba.”

  9. Ya mai da ikkilisiya ta zama mai tsarki ta wurin ikon maganarsa, ya kuma tsabtacce ta ta wurin wanke ta da ruwa.

  10. Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan.

  11. Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.

  12. Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah.

  13. Muna kuma gode wa Allah ba fasawa domin, sa’ad da kuka karɓi maganar Allah, wadda kuka ji daga gare mu, kun karɓe ta ba kamar maganar mutane ba, sai dai kamar yadda take, maganar Allah wadda take aiki a cikinku ku da kuka ba da gaskiya.

  14. da kuma yadda tun kana ɗan jinjiri ka san Nassosi masu tsarki, waɗanda suke iya sa ka zama mai hikima zuwa ceto ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu.

  15. Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci,

  16. domin mutumin Allah yă zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki.

  17. Kamar dai yadda Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Yau, in kuka ji muryarsa,

  18. Maganar Allah tana da rai, tana kuma da ƙarfin aiki. Ta fi kowane takobi mai baki biyu kaifi. Maganarsa takan ratsa har ciki-ciki, tana raba rai da ruhu, gaɓoɓi da kuma ɓargon ƙashi; har sai ta tone ainihi wane ne muke.

  19. Ya zaɓa yă haife mu ta wurin kalmar gaskiya, domin mu zama ’ya’yan fari na dukan abin da ya halitta.

  20. Saboda haka, ku rabu da ƙazamin hali da kuma kowace irin mugunta ku kuma yi na’am da maganar da aka shuka a cikinku da tawali’u, wadda za tă iya cetonku.

  21. Kada ku zama masu ji kawai, ku ruɗi kanku. A maimakon haka ku zama masu yin abin da ta ce.

  22. Duk wanda yake ji magana ne kawai, bai kuwa aikata abin da ta ce ba, yana kama da mutumin da ya kalli fuskarsa a madubi

  23. Amma duk mai duba cikakkiyar ƙa’idan nan ta ’yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai yă mance ba, sai dai mai yi ne yă zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake yi.

  24. gama a rubuce yake cewa, “Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne.”

  25. Gama an sāke haihuwarku, ba da iri da yake lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, ta wurin rayayyiya da kuma madawwamiyar maganar Allah.