Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Scriptures: Reveal the laws, statutes, and judgments of God

4 ayoyi · 108 fannoni

Ayoyi game da Reveal the laws, statutes, and judgments of God

  1. Sa’ad da Musa ya tafi ya faɗa wa mutanen duk kalmomin Ubangiji da dokokinsa, sai suka amsa da murya ɗaya suna cewa, “Duk abin da Ubangiji ya faɗa, za mu yi.”

  2. Sai Musa ya rubuta duk abin da Ubangiji ya faɗa. Ya tashi kashegari da sassafe ya gina bagade kusa da dutsen, ya aza al’amudai goma sha biyu bisa ga kabilu goma sha biyu na Isra’ila.

  3. Ga shi, na koya muku ƙa’idodi da dokoki, yadda Ubangiji Allahna ya umarce ni, don ku bi su a ƙasar da za ku shiga ku mallaki.

  4. Sa’an nan Ubangiji ya umarce ni a wannan lokaci, in koya muku ƙa’idodi da dokokin da za ku bi a ƙasar da kuke hayewa Urdun don mallake.