Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Scriptures

159 ayoyi · 108 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad da Musa ya tafi ya faɗa wa mutanen duk kalmomin Ubangiji da dokokinsa, sai suka amsa da murya ɗaya suna cewa, “Duk abin da Ubangiji ya faɗa, za mu yi.”

  2. Sai Musa ya rubuta duk abin da Ubangiji ya faɗa. Ya tashi kashegari da sassafe ya gina bagade kusa da dutsen, ya aza al’amudai goma sha biyu bisa ga kabilu goma sha biyu na Isra’ila.

  3. Kada ku ƙara, kada ku rage daga cikin abin da nake umarce ku. Amma ku kiyaye umarnan nan na Ubangiji Allahnku, da na ba ku.

  4. Ga shi, na koya muku ƙa’idodi da dokoki, yadda Ubangiji Allahna ya umarce ni, don ku bi su a ƙasar da za ku shiga ku mallaki.

  5. Sa’an nan Ubangiji ya umarce ni a wannan lokaci, in koya muku ƙa’idodi da dokokin da za ku bi a ƙasar da kuke hayewa Urdun don mallake.

  6. Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku.

  7. Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.

  8. Ya ƙasƙantar da ku, ya bar ku da yunwa, sa’an nan ya ciyar da ku da Manna, wadda ku, ko kakanninku, ba su sani ba, ta haka ne ya sa kuka sani cewa, ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba, amma ta wurin kowace kalmar da ta fito daga bakin Ubangiji.

  9. Saboda haka, sai ku riƙe waɗannan kalmomina gam a zukatanku da ranku; ku ɗaura su kamar alama a hannuwanku, da goshinku.

  10. Ku koyar da su ga ’ya’yanku, ku yi ta haddace su, sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.

  11. Ku lura, ku aikata dukan abin da na umarce ku; kada ku ƙara, kada ku rage daga cikin.

  12. Zai kasance tare da shi, zai kuma karanta shi dukan kwanakin ransa, saboda yă koyi girmama Ubangiji Allahnsa, yă kuma bi dukan kalmomin wannan doka da kuma waɗannan ƙa’idodi a hankali

  13. don kada yă ɗauki kansa ya fi ’yan’uwansa, yă kuma juya daga dokar zuwa dama, ko zuwa hagu. Sa’an nan shi da kuma zuriyarsa za su daɗe suna mulki a Isra’ila.

  14. sa’ad da dukan Isra’ila suka zo, don su bayyana a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da zai zaɓa, za ku karanta wannan doka a gabansu, a kunnuwansu.

  15. Ku tattara mutane, maza, mata da kuma yara, da baƙin da suke zama a cikin garuruwanku, saboda su saurara, su kuma koyi tsoron Ubangiji Allahnku, su lura, su bi dukan kalmomin wannan doka.

  16. ’Ya’yansu, waɗanda ba su san wannan doka ba, dole su ji ta, su kuma koyi tsoron Ubangiji Allahnku muddin ranku a ƙasar da kuke haye Urdun ku ci gādonta.”

  17. A shekara ta uku ta mulkinsa, ya aiki ma’aikatansa Ben-Hayil, Obadiya, Zakariya, Netanel da Mikahiya su yi koyarwa a garuruwan Yahuda.

  18. Tare da su akwai waɗansu Lawiyawa, Shemahiya, Netaniya, Zebadiya, Asahel, Shemiramot, Yehonatan, Adoniya, Tobiya da Tob Adoniya, da kuma firistoci Elishama da Yehoram.

  19. Suka yi koyarwa a dukan Yahuda, suna ɗauke da Littafin Dokar Ubangiji tare da su; suka tafi ko’ina a dukan garuruwan Yahuda suka koyar da mutane.

  20. sai dukan mutane suka taru kamar mutum guda a dandali a gaban Ƙofar Ruwa. Suka faɗa wa Ezra malamin Doka yă fitar da Littafin Dokar Musa, wanda Ubangiji ya umarta domin Isra’ila.

  21. Ya karanta Dokar da ƙarfi daga safe har tsakar rana yayinda yake a kan dandali da yake fuskantar dandali a gaban Ƙofar Ruwa, gaban maza, mata da kuma sauran mutanen da za su iya fahimta. Dukan mutane kuwa suka saurara a hankali ga karatun Littafin Dokar.

  22. Lawiyawa, wato, su Yeshuwa, Bani, Sherebiya, Yamin, Akkub, Shabbetai, Hodiya, Ma’asehiya, Kelita, Azariya, Yozabad, Hanan da Felahiya, suka koyar da mutane a cikin Dokar yayinda mutane suke a tsaye a can.

  23. Suka karanta daga Littafin Dokar Allah, suna sa kowa ya gane, suna kuma ba da fassarar domin mutane su fahimci abin da ake karatu.

  24. Ban fasa bin dokokin da ya bayar ba; na riƙe maganarsa da muhimmanci fiye da abincin yau da gobe.

  25. Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji, kuma yana ta nazarinta dare da rana.