Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Servants

291 ayoyi · 147 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai ya ce, “Ranka yă daɗe sarki, da yake bawanka gurgu ne, na ce, ‘A sa mini sirdi a kan jakina don in hau in tafi tare da sarki.’ Amma Ziba bawana ya bashe ni.

  2. Amma bayan shekaru uku, biyu daga cikin bayin Shimeyi suka gudu zuwa wurin Akish ɗan Ma’aka, sarkin Gat. Aka faɗa wa Shimeyi cewa, “Bayinka suna a Gat.”

  3. Haka ma Yerobowam, ɗan Nebat, shi ma ya yi wa sarki tawaye. Shi ɗaya ne daga shugabannin Solomon, shi mutumin Efraim ne daga Zereda, mahaifiyarsa kuwa gwauruwa ce, mai suna Zeruwa.

  4. Zimri, ɗaya daga cikin shugabanni, wanda ya shugabanci rabin kekunan yaƙin Ela, ya yi maƙarƙashiya a kansa. Ela yana a Tirza a lokacin, ya bugu a gidan Arza, sarkin fada a Tirza.

  5. Saye da tufafin makoki kewaye a gindinsu, da kuma igiyoyi kewaye da kawunansu, suka tafi wurin sarkin Isra’ila, suka ce, “Bawanka Ben-Hadad ya ce, ‘Ina roƙonka bari in rayu.’ ” Sarki ya amsa, “Har yanzu yana da rai? Shi ɗan’uwana ne.”

  6. Matar wani daga ƙungiyar annabawa ta yi wa Elisha kuka ta ce, “Mijina, bawanka, ya mutu, ka kuma san yadda ya girmama Ubangiji. Amma ga shi yanzu mai binsa bashi ya zo yă kwashe ’ya’yana maza biyu su zama bayinsa.”

  7. To, daga cikin hare haren da mutanen Aram suke kaiwa, sai suka kama wata yarinya daga ƙasar Isra’ila, aka sa ta zama mai yi wa matar Na’aman aiki.

  8. Sai ta ce wa uwargijiyarta, “Da dai shugabana zai ga annabin da yake Samariya, da annabin zai warkar da shi daga kuturtarsa.”

  9. Sai Na’aman ya je wurin maigidansa ya faɗa masa abin da yarinyan nan daga Isra’ila ta faɗa.

  10. Sai bayin Na’aman suka je kusa da shi suka ce, “Baba, da a ce annabin ya ce ka yi wani abu mai wuya, da ba za ka yi ba? Balle fa cewa kawai ya yi, ‘Ka yi wanka ka kuma tsarkaka’!”

  11. sai Gehazi, bawan Elisha mutumin Allah, ya yi tunani a ransa ya ce, “Maigidana ya yi wa Na’aman mutumin Aram nan ƙaramci da bai karɓi duk abin da ya kawo ba. Muddin Ubangiji yana a raye, zan bi shi a guje in karɓi wani abu daga gare shi.”

  12. Gehazi ya amsa ya ce, “Lafiya ƙalau. Maigidana ne ya aiko ni cewa, ‘Samari biyu daga ƙungiyar annabawa sun ziyarce ni daga ƙasa mai duwatsu na yankin Efraim. Ina roƙonka ka ba su talenti na azurfa da tufafi kashi biyu.’ ”

  13. Da Gehazi ya isa wani tudu, sai ya karɓi kayan daga wurin bayin ya shiga da su a ɓoye a cikin gida. Sa’an nan ya sallami mutanen suka tafi.

  14. Fadawan Amon suka ƙulla maƙarƙashiya suka kashe shi a cikin fadarsa.

  15. Sheshan ba shi da ’ya’ya maza, sai ’ya’ya mata kawai. Yana da bawa mutumin Masar mai suna Yarha.

  16. Sheshan ya ba da ’yarsa aure ga bawansa Yarha, ta kuwa haifa masa Attai.

  17. Daga wannan rana zuwa gaba, rabin mutane suka yi aiki, yayinda sauran rabin suka kintsa da māsu, da garkuwa, da bakkuna da makamai. Shugabanni suka goyi bayan dukan mutanen Yahuda

  18. Saboda haka ni, da ’yan’uwana, da bayina, da matsaran da suke tare da ni, ba wanda ya tuɓe tufafinsa; kowa ya rataye makaminsa, ko ya je shan ruwa ma.

  19. Har illa yau waɗansu suka ce, “Mun ci bashin kuɗi don mu biya haraji a kan gonakinmu, da gonakin inabinmu.

  20. Ga shi kuwa, mu da su dangin juna ne, ’ya’yanmu da nasu kuma ɗaya ne, duk da haka an tilasta mu mu sa ’ya’yanmu mata da maza su zama bayi. Har ma an riga an bautar waɗansu daga cikin ’ya’yanmu mata, amma ba mu da iko mu ce kome, domin gonakinmu da gonakin inabinmu suna a hannun waɗansu mutane.”

  21. “Mutum bai sha wahalar aiki ba a duniya? Rayuwarsa ba kamar ta wanda aka yi hayarsa ba ne?

  22. Kamar yadda bawa yakan jira yamma ta yi, ko kuma kamar yadda wanda aka yi hayarsa yakan jira a biya shi kuɗin aikin da ya yi.

  23. Na kira bawana, amma bai amsa ba, ko da yake na roƙe shi da bakina.

  24. Hadaya da sadaka ba ka sha’awa, amma kunnuwana ka huda; hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka bukata.

  25. Idanuna za su kasance a kan amintattu a cikin ƙasar, don su zauna tare da ni; tafiyarsa ba ta da zargi zai yi mini hidima.