Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Servants

291 ayoyi · 147 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “ ‘Duk wanda ba daga cikin iyalin firistoci ba, ko da yake yana zama tare da su, ko kuwa an ɗauke shi yana yin musu aiki, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun hadayun ba.

  2. Duk abin da gonar ta ba da amfani a shekara ta Asabbaci, zai zama abinci gare ku, wa kanku, bayinku maza da mata, da ma’aikatan da kuka ɗauka aiki, da kuma waɗanda ba zama ɗinɗinɗin suke yi tare da ku ba,

  3. Ku keɓe shekara ta hamsin ku kuma yi shelar ’yanci a dukan ƙasar ga mazaunanta. Za tă zama shekarar murna gare ku; kowannenku zai koma ga mallakar iyalinsa, kuma kowa ga danginsa.

  4. “ ‘In ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku ya talauta a cikinku, ya kuma sayar da kansa gare ku, kada ku sa yă yi kamar bawa.

  5. Amma a ɗauke shi a matsayin ma’aikacin da aka ɗauka aiki, ko mazaunan da ba na ɗinɗinɗin ba a cikinku, sai yă yi muku aiki sai Shekara ta Murna.

  6. Sa’an nan a sake shi da ’ya’yansa, yă kuma koma ga danginsa da mallakar kakanninsa.

  7. “ ‘Bayinku maza da mata, za su zo daga al’ummai da suke kewaye da ku, daga gare su za ku iya saya bayi.

  8. Za ku iya saya waɗansu mutanen da ba sa zama ɗinɗinɗin a cikinku, da kuma membobin danginsu da aka haifa a ƙasarku.

  9. Za ku iya ba da su ga ’ya’yanku a matsayin kayan gādo, za ku kuma iya mai da su bayi dukan rayuwarsu, amma kada ku yi mulki a bisa ’yan’uwanku Isra’ilawa da tsanani.

  10. “ ‘In baƙo, ko wani da yake zama ba na ɗinɗinɗin ba a cikinku, ya wadace, ɗaya daga cikin mutanen ƙasarku kuwa ya talauta, ya kuma sayar da kansa ga baƙon da yake zama a cikinku, ko memba na dangin baƙon,

  11. yana da izini samun fansa, bayan ya sayar da kansa. Ɗaya daga cikin danginsa zai iya fansarsa.

  12. Kawu ko yaron ɗan’uwan mahaifin wannan mutum, ko kuwa wani dangi a cikin zuriyarsa, zai iya fanshe shi. Ko kuma in ya azurta, zai iya fansar kansa.

  13. Da shi da mai sayansa, za su ƙirga lokaci daga shekarar da ya sayar da kansa har zuwa Shekara ta Murna. Farashin sakinsa zai dangana a kuɗin da ake biyan ma’aikacin da aka ɗauka aiki, na yawan shekarun ne.

  14. In shekaru sun ragu, dole yă biya don fansarsa da kuɗi mai yawa fiye da wanda aka saye shi.

  15. In shekarun sun rage kaɗan ne kafin Shekara ta Murna, sai yă yi lissafin wannan, yă kuma biya fansarsa daidai wa daida.

  16. Sai a yi da shi kamar ma’aikacin da aka ɗauka aiki, daga shekara zuwa shekara; dole ku tabbata mai shi bai mallake shi da tsanani ba.

  17. “ ‘Ko ma ba a fanshe shi a ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyi ba, sai a sake shi da ’ya’yansa a Shekara ta Murna,

  18. gama Isra’ilawa nawa ne a matsayin bayi. Su bayina ne waɗanda na saya daga Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.

  19. Kada ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka. Kada kuma ka yi sha’awar gidan maƙwabcinka, ko gonarsa, ko bayinsa maza da mata, ko saniyarka, ko jakinsa, ko dai wani abin da yake na maƙwabtanka.”

  20. A maimakon haka, sai ku ci su a gaban Ubangiji Allahnku a wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa, da ku da ’ya’yanku maza da mata, da bayinku maza da mata, da kuma Lawiyawa daga biranenku, ku kuwa yi farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku a kowane abin da kuka sa hannunku.

  21. In ɗan’uwa mutumin Ibraniyawa, namiji ko ta mace, ya sayar da kansa gare ka, ya kuma bauta maka shekaru shida, a shekara ta bakwai dole ka ’yantar da shi.

  22. Sa’ad da kuka sake shi, kada ku bar shi yă tafi hannu wofi.

  23. Ku ba shi kyautai hannu sake daga tumakinku, daga masussukarku, da kuma daga wurin matsewar inabinku. Ku ba shi yadda Ubangiji Allahnku ya albarkace ku.

  24. Amma in bawanka ya ce maka, “Ba na so in bar ka,” saboda yana ƙaunarka da iyalinka, ya kuma fiye masa yă zauna da kai,

  25. sai ka ɗauki basilla ka huda kunnensa a bakin ƙofa, zai kuwa zama bawanka dukan rayuwarsa. Ka yi haka ma wa baiwarka.