- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Servants: Eliezer
Ayoyi game da Eliezer
Yanzu fa Ibrahim ya tsufa, yana da shekaru masu yawa, Ubangiji kuma ya albarkace shi a kowace hanya.
Sai Ibrahim ya ce wa babban bawan gidansa, wanda yake lura da duk abin da yake da shi, “Sa hannunka a ƙarƙashin cinyata.
Ina so ka rantse da sunan Ubangiji Allah na sama da ƙasa, cewa ba za ka samo wa ɗana mata daga ’yan matan Kan’aniyawa, waɗanda nake zama cikinsu ba.
Amma za ka tafi ƙasata da kuma cikin ’yan’uwana, ka samo mata saboda ɗana Ishaku.”
Bawan ya ce masa, “Me zai faru in matar ba tă yarda tă zo tare da ni zuwa wannan ƙasa ba? In komar da ɗanka a ƙasar da ka fito ne ke nan?”
Ibrahim ya ce, “Ka tabbata ba ka komar da ɗana can ba.”
Ubangiji Allah na sama, wanda ya fitar da ni daga gidan mahaifina, da kuma ƙasar asalina wanda kuma ya yi magana da ni, ya yi mini alkawari da rantsuwa cewa, “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa, zai aika mala’ikansa yă sha gabanka domin ka samo wa ɗana mata daga can.
In matar ba tă yarda tă zo tare da kai ba, za a kuɓutar da kai daga wannan rantsuwa. Sai dai kada ka kai ɗana a can.”
Saboda haka bawan ya sa hannunsa a ƙarƙashin cinyar maigidansa Ibrahim, ya kuma rantse masa game da wannan al’amari.
Sai bawan ya ɗibi raƙuma goma na maigidansa ya tafi, ɗauke da kowane irin abubuwa masu kyau daga wurin maigidansa. Ya fita don yă tafi Aram-Naharayim, ya kama hanyarsa zuwa garin Nahor.
Ya sa raƙuman suka durƙusa kusa da rijiya a bayan gari; wajen yamma ne, lokacin da mata sukan fita ɗiban ruwa.
Sai ya yi addu’a ya ce, “Ya Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim, ka ba ni nasara yau, ka kuma nuna alheri ga maigidana Ibrahim.
Duba, ina tsaye a bakin rijiyar ruwa, ’ya’ya matan mutanen gari kuma suna fitowa domin ɗiban ruwa.
Bari yă zama sa’ad da na ce wa wata yarinya, ‘Ina roƙonki ki saukar da tulunki domin in sha,’ in ta ce, ‘Ka sha, zan kuma ba wa raƙumanka ma’; bari tă zama ita ce ka zaɓa wa bawanka Ishaku. Ta haka zan san cewa ka nuna wa maigidana alheri.”
Kafin ya gama addu’a, sai Rebeka ta fito da tulu a kafaɗarta. Ita ’yar Betuwel ɗan Milka, matar Nahor, ɗan’uwan Ibrahim.
Yarinyar kuwa kyakkyawa ce, budurwa, ba namijin da ya taɓa kwana da ita. Ta gangara zuwa rijiyar, ta cika tulunta ta kuma hauro.
Bawan ya yi sauri ya same ta ya ce, “Ina roƙonki ki ba ni ɗan ruwa daga tulunki.”
Ta ce, “Ka sha, ranka yă daɗe,” ta yi sauri ta saukar da tulun a hannuwanta, ta kuma ba shi, ya sha.
Bayan ta ba shi ya sha, sai ta ce, “Zan ɗebo wa raƙumanka ruwa su ma, har sai sun gama sha.”
Sai ta yi sauri ta juye ruwan da yake tulunta cikin kwami, ta koma zuwa rijiyar da gudu don ta ƙara ɗebo ruwa, ta kuma ɗebo isashe saboda dukan raƙumansa.
Mutumin bai ce uffam ba, ya dai kalle ta sosai don yă san ko Ubangiji ya ba shi nasara a tafiyarsa ko babu.
Sa’ad da raƙuman suka gama shan ruwa, mutumin ya fitar da zoben hanci na zinariya mai nauyin giram biyar da woroworo biyu na zinariya masu nauyin shekel goma, ya ba ta.
Sa’an nan ya tambaye ta ya ce, “Ke ’yar wace ce? Ina roƙonki ki faɗa mini, akwai wuri a gidan mahaifinki da za mu kwana?”
Sai ta ce masa, “Ni ’yar Betuwel ce ɗan da Milka ta haifa wa Nahor.”
Ta ƙara da cewa, “Muna da isashen ciyawa da abincin dabbobi, da kuma wuri domin ku kwana.”