Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Servants: To be anxious for their welfare

6 ayoyi · 147 fannoni

Ayoyi game da To be anxious for their welfare

  1. Ɗaya daga cikin bayin Nabal ya gaya wa Abigiyel matar Nabal cewa, “Dawuda ya aiko da bayinsa daga jeji su gai da maigida, amma maigida ya zazzage su.

  2. Waɗannan mutane kuwa sun yi mana kirki ƙwarai, ba su ba mu wata wahala ba. Babu abu guda da ya ɓace mana dukan lokacin da muke tare da su.

  3. Dare da rana sun zama mana katanga kewaya da mu, a duk tsawon lokacin da muke kiwon tumakinmu kusa da su.

  4. Ki yi nazari a kai, ki ga ko za ki iya yin wani abu, domin masifa yana nan rataye a wuyan maigidanmu da dukan iyalin gidansa. Shi mugun mutum ne wanda ba wani da zai iya yin masa magana.”

  5. To, daga cikin hare haren da mutanen Aram suke kaiwa, sai suka kama wata yarinya daga ƙasar Isra’ila, aka sa ta zama mai yi wa matar Na’aman aiki.

  6. Sai ta ce wa uwargijiyarta, “Da dai shugabana zai ga annabin da yake Samariya, da annabin zai warkar da shi daga kuturtarsa.”