Tsallake zuwa abun ciki

Rebekah

29 ayoyi · 5 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Rebekah

  1. Betuwel ya haifi Rebeka. Milka ta haifa wa Nahor ɗan’uwan Ibrahim waɗannan ’ya’ya maza takwas.

  2. Kafin ya gama addu’a, sai Rebeka ta fito da tulu a kafaɗarta. Ita ’yar Betuwel ɗan Milka, matar Nahor, ɗan’uwan Ibrahim.

  3. Rebeka fa tana da wani ɗan’uwa mai suna Laban, sai ya yi hanzari ya fita zuwa wurin mutumin a rijiyar.

  4. Nan da nan da ya ga zoben hancin da woroworo a hannuwan ’yar’uwansa, ya kuma ji Rebeka ta faɗa abin da mutumin ya ce mata, sai ya fita zuwa wurin mutumin, ya same shi yana tsaye wajen raƙuma kusa da rijiyar.

  5. “Kafin in gama addu’ar, a zuciyata, sai ga Rebeka ta fito da tulunta a kafaɗarta. Ta gangara zuwa rijiyar ta ɗebo ruwa, na kuma ce mata, ‘Ina roƙonki ki ba ni ɗan ruwa daga tulunki.’

  6. Ga Rebeka, ɗauke ta ku tafi, bari tă zama matar ɗan maigidanka, yadda Ubangiji ya umarta.”

  7. Sa’an nan bawan ya fito da kayan ado na zinariya da azurfa da kayayyaki na tufafi ya ba wa Rebeka; ya kuma ba wa ɗan’uwanta da mahaifiyarta kyautai masu tsada.

  8. Saboda haka suka kira Rebeka suka ce mata, “Za ki tafi tare da mutumin nan?” Sai ta ce, “Zan tafi.”

  9. Saboda haka suka sallame Rebeka, ’yar’uwarsu, duk da uwar goyonta da bawan Ibrahim da mutanensa.

  10. Suka kuma albarkaci Rebeka suka ce mata, “’Yar’uwarmu, bari ki zama mahaifiyar dubu dubbai, bari zuriyarki su mallaki ƙofofin abokan gābansu.”

  11. Sa’an nan Rebeka da bayinta mata suka shirya suka hau raƙumansu suka koma tare da mutumin. Da haka bawan ya ɗauki Rebeka ya tafi.

  12. Rebeka ma ta ɗaga ido sai ta ga Ishaku. Ta sauka daga raƙuminta da sauri,

  13. Ishaku ya kawo ta cikin tentin mahaifiyarsa Saratu, ya kuma auri Rebeka. Ta haka ta zama matarsa, ya kuwa ƙaunace ta; Ishaku kuma ya ta’azantu bayan rasuwar mahaifiyarsa.

  14. Ishaku yana da shekara arba’in sa’ad da ya auri Rebeka ’yar Betuwel, mutumin Aram, daga Faddan Aram, ’yar’uwar Laban mutumin Aram.

  15. Ishaku ya yi addu’a ga Ubangiji a madadin matarsa, saboda ba ta haihuwa. Ubangiji ya amsa addu’arsa, matarsa Rebeka kuwa ta yi ciki.

  16. Ishaku, mai son ci naman jeji, ya ƙaunaci Isuwa, amma Rebeka ta ƙaunaci Yaƙub.

  17. Sa’ad da mutanen wurin suka tambaye shi game da matarsa, sai ya ce, “’Yar’uwata ce,” gama yana tsoro yă ce, “Ita matata ce.” Ya yi tunani, “Mutane wannan wuri za su kashe ni ta dalili Rebeka, domin kyakkyawa ce.”

  18. Sa’ad da Ishaku ya daɗe a can, sai Abimelek sarkin Filistiyawa ya duba daga taga ya ga Ishaku yana rungumar matarsa Rebeka.

  19. Su ne suka zama sanadin baƙin ciki ga Ishaku da Rebeka.

  20. Ashe, Rebeka tana ji sa’ad da Ishaku ya yi wa ɗansa Isuwa magana. Da Isuwa ya tafi jeji don yă farauto nama yă kawo,

  21. sai Rebeka ta ce wa ɗanta Yaƙub, “Ka ji nan, na ji mahaifinka ya ce wa ɗan’uwanka Isuwa,

  22. Yaƙub ya ce wa mahaifiyarsa Rebeka, “Amma ɗan’uwana Isuwa mutum ne mai gashi a jiki, ni kuma jikina sumul yake.

  23. Sa’an nan Rebeka ta ɗauki riguna mafi kyau na Isuwa babban ɗanta, waɗanda take da su a gida ta sa wa ƙaramin ɗanta Yaƙub.

  24. Sa’ad da aka faɗa wa Rebeka abin da babban ɗanta Isuwa ya faɗa, sai ta kira ɗanta Yaƙub ta ce masa, “Ɗan’uwanka Isuwa yana ta’azantar da kansa da tunanin kashe ka.

  25. Sa’an nan Rebeka ta ce wa Ishaku, “Ni fa na gaji da matan Hittiyawan nan. In Yaƙub ya auri mata daga cikin matan ƙasan nan, wato, daga matan Hittiyawa irin waɗannan, rayuwata ba za tă daɗa mini kome ba.”