Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Rebekah

106 ayoyi · 9 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Bayan wani ɗan lokaci, sai aka faɗa wa Ibrahim cewa, “Ga shi, Milka ita ma ta haifa wa Nahor ɗan’uwanka, ’ya’ya maza;

  2. ɗan fari shi ne Uz, ɗan’uwansa kuma Buz, Kemuwel (shi ne mahaifin Aram),

  3. Kesed, Hazo, Fildash; Yidlaf, da kuma Betuwel.”

  4. Betuwel ya haifi Rebeka. Milka ta haifa wa Nahor ɗan’uwan Ibrahim waɗannan ’ya’ya maza takwas.

  5. Kafin ya gama addu’a, sai Rebeka ta fito da tulu a kafaɗarta. Ita ’yar Betuwel ɗan Milka, matar Nahor, ɗan’uwan Ibrahim.

  6. Yarinyar kuwa kyakkyawa ce, budurwa, ba namijin da ya taɓa kwana da ita. Ta gangara zuwa rijiyar, ta cika tulunta ta kuma hauro.

  7. Bawan ya yi sauri ya same ta ya ce, “Ina roƙonki ki ba ni ɗan ruwa daga tulunki.”

  8. Ta ce, “Ka sha, ranka yă daɗe,” ta yi sauri ta saukar da tulun a hannuwanta, ta kuma ba shi, ya sha.

  9. Bayan ta ba shi ya sha, sai ta ce, “Zan ɗebo wa raƙumanka ruwa su ma, har sai sun gama sha.”

  10. Sai ta yi sauri ta juye ruwan da yake tulunta cikin kwami, ta koma zuwa rijiyar da gudu don ta ƙara ɗebo ruwa, ta kuma ɗebo isashe saboda dukan raƙumansa.

  11. Mutumin bai ce uffam ba, ya dai kalle ta sosai don yă san ko Ubangiji ya ba shi nasara a tafiyarsa ko babu.

  12. Sa’ad da raƙuman suka gama shan ruwa, mutumin ya fitar da zoben hanci na zinariya mai nauyin giram biyar da woroworo biyu na zinariya masu nauyin shekel goma, ya ba ta.

  13. Sa’an nan ya tambaye ta ya ce, “Ke ’yar wace ce? Ina roƙonki ki faɗa mini, akwai wuri a gidan mahaifinki da za mu kwana?”

  14. Sai ta ce masa, “Ni ’yar Betuwel ce ɗan da Milka ta haifa wa Nahor.”

  15. Ta ƙara da cewa, “Muna da isashen ciyawa da abincin dabbobi, da kuma wuri domin ku kwana.”

  16. Sa’an nan mutumin ya rusuna ya yi wa Ubangiji sujada,

  17. yana cewa, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim, wanda bai daina nuna alheri da amincinsa ga maigidana ba. Ni kam, Ubangiji ya bishe ni a tafiyata zuwa gidan ’yan’uwan maigidana.”

  18. Yariyan ta gudu ta faɗa wa mutanen gidan mahaifiyarta game da abubuwan nan.

  19. Rebeka fa tana da wani ɗan’uwa mai suna Laban, sai ya yi hanzari ya fita zuwa wurin mutumin a rijiyar.

  20. Nan da nan da ya ga zoben hancin da woroworo a hannuwan ’yar’uwansa, ya kuma ji Rebeka ta faɗa abin da mutumin ya ce mata, sai ya fita zuwa wurin mutumin, ya same shi yana tsaye wajen raƙuma kusa da rijiyar.

  21. Sai ya ce, “Zo, ya kai mai albarka na Ubangiji, don me kake tsaye a waje? Gama na shirya gida da wuri domin raƙuma.”

  22. Don haka mutumin ya tafi gidan, aka kuma saukar da kaya kan raƙuman. Aka kawo wa raƙuman ciyawa da abincin dabbobi, aka kuma kawo ruwa dominsa da mutanensa su wanke ƙafafunsu.

  23. Sa’an nan aka ajiye abinci a gabansa, amma ya ce, “Ba zan ci ba, sai na faɗi abin da yake tafe da ni.” Sai Laban ya ce, “Faɗa mana.”

  24. Saboda haka ya ce, “Ni bawan Ibrahim ne.

  25. Ubangiji ya albarkaci maigidana sosai, ya kuma zama mai arziki. Ya ba shi tumaki, shanu, azurfa, zinariya, bayi maza da mata, raƙuma, da kuma jakuna.