Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Rebekah

106 ayoyi · 9 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. To, fa, ɗana, yi abin da na ce; gudu nan take zuwa wurin ɗan’uwana Laban a Haran.

  2. Zauna tare da shi na ɗan lokaci sai ɗan’uwanka ya huce.

  3. Sa’ad da ɗan’uwanka ya daina fushi da kai, ya kuma manta da abin da ka yi masa, zan aika don ka dawo daga can. Don me zan rasa ku biyu a rana guda?”

  4. Sa’an nan Rebeka ta ce wa Ishaku, “Ni fa na gaji da matan Hittiyawan nan. In Yaƙub ya auri mata daga cikin matan ƙasan nan, wato, daga matan Hittiyawa irin waɗannan, rayuwata ba za tă daɗa mini kome ba.”

  5. A can aka binne Ibrahim da matarsa Saratu, a can aka binne Ishaku da matarsa Rebeka, a can kuma na binne Liyatu.

  6. Ba ma haka kaɗai ba, ’ya’yan Rifkatu suna da mahaifi guda ne, wato, mahaifinmu Ishaku.