Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prophets

655 ayoyi · 128 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai na yi tambaya na ce, “Mene ne waɗannan ranka yă daɗe?” Mala’ikan da yake magana da ni ya amsa ya ce, “Zan nuna maka mene ne su.”

  2. Sai Ubangiji ya yi wa mala’ikan da ya yi magana da ni magana da kalmomi masu daɗi da kuma masu ta’azantarwa.

  3. Sai mala’ikan da yake magana da ni ya ce, “Ka yi shelar maganan nan, ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Ina kishi domin Urushalima da Sihiyona,

  4. Na tambayi mala’ikan da yake mini magana, na ce, “Mene ne waɗannan?” Ya amsa mini ya ce, “Waɗannan su ne ƙahonin da suka watsar da Yahuda, Isra’ila da kuma Urushalima.”

  5. Ba shakka zan tā da hannuna a kansu domin bayinsu su washe su. Sa’an nan za ku san cewa Ubangiji Maɗaukaki ne ya aiko ni.

  6. Suka taurare zukatansu kamar dutse, suka ƙi jin abin da doka ko kuma maganar Ubangiji Maɗaukaki take faɗi wadda ya aika ta wurin Ruhunsa ta wurin annabawan farko. Saboda haka Ubangiji Maɗaukaki ya ji fushi ƙwarai.

  7. “A ranan nan kowane annabi zai ji kunyar annabcin wahayinsa. Ba zai sa rigar annabci mai gashi ba don yă yi ruɗu.

  8. Annabci, wannan ita ce maganar Ubangiji ga Isra’ila ta wurin Malaki.

  9. Tufafin Yohanna kuwa an yi su da gashin raƙumi ne, yana kuma daure da ɗamara ta fata. Abincinsa kuwa fāri ne da zumar jeji.

  10. Ku yi murna ku kuma yi farin ciki, domin ladarku mai yawa ne a sama, gama haka suka tsananta wa annabawan da suka riga ku.

  11. Sai ya amsa ya ce, “Mugaye da masu zinan zamanin nan suna neman wata alama mai banmamaki! Amma babu wadda za a nuna musu, sai dai alama ta annabi Yunana.

  12. Sai suka ji haushinsa. Amma Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa da kuma a gidansa na kaɗai annabi ba ya samun girma.”

  13. Saboda haka ina aika muku da annabawa, da masu hikima da malamai. Waɗansunsu za ku kashe ku kuma gicciye; waɗansu kuma za ku yi musu bulala a majami’unku kuna kuma binsu gari-gari.

  14. Ta haka alhakin jinin masu adalcin da aka zubar a duniya, tun daga jinin Habila mai adalci, zuwa jinin Zakariya ɗan Berekiya, wanda kuka kashe tsakanin haikali da bagade zai koma kanku.

  15. Gaskiya nake gaya muku, duk wannan zai auko wa wannan zamani.

  16. “Urushalima, ayya Urushalima, ke da kike kashe annabawa, kike kuma jifan waɗanda aka aiko gare ki, sau da sau na so in tattara ’ya’yanki wuri ɗaya, yadda kaza takan tattara ’ya’yanta cikin fikafikanta, amma kuka ƙi.

  17. Ga shi, an bar muku gidanku a yashe.

  18. “Saboda haka sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama mai kawo hallaka,’wanda annabi Daniyel ya yi magana a kai, yana tsaye a tsattsarkan wuri (mai karatu yă gane),

  19. Suna haurawa a hanyarsu zuwa Urushalima ke nan, Yesu yana a gaba, almajiran suna bin sa suna mamaki, waɗanda suke bi kuma suna ji tsoro. Ya sāke kai Sha Biyun nan gefe, ya gaya musu abin da zai faru da shi.

  20. Ya ce, “Za mu haura zuwa Urushalima, za a bashe Ɗan Mutum, ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa, a kuma ba da shi ga Al’ummai,

  21. waɗanda za su yi masa ba’a, su tofa masa miyau, su yi masa bulala, su kuma kashe shi. Bayan kwana uku kuma yă tashi.”

  22. Har yanzu ya sāke aikan wani. Wannan kuwa suka kashe. Ya aika waɗansu da yawa; suka bubbuge waɗansu, sauran kuwa suka kashe.

  23. Dawuda da kansa ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce, “ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana sai na sa abokan gābanka a ƙarƙashin sawunka.” ’

  24. gama zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba kuwa zai taɓa shan ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun haihuwa.

  25. Da Elizabet ta ji gaisuwar Maryamu, sai jaririn da yake a cikinta ya yi motsi. Elizabet kuma ta cika da Ruhu Mai Tsarki.