Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prophets: Often endued with miraculous power

11 ayoyi · 128 fannoni

Ayoyi game da Often endued with miraculous power

  1. Musa ya amsa ya ce, “In ba su gaskata ni ba, suka kuma ce, ‘Ubangiji bai bayyana gare ka ba fa’?”

  2. Sai Ubangiji ya ce, “Mene ne wannan a hannunka?” Musa ya amsa ya ce, “Sanda.”

  3. Sai Ubangiji ya ce, “Jefa shi ƙasa.” Musa ya jefa shi ƙasa, sai sandan ya zama maciji, Musa kuwa ya gudu daga gare shi.

  4. Sai Ubangiji ya ce masa, “Sa hannunka ka ɗauke shi ta wutsiya.” Sai Musa ya miƙa hannu, ya kama macijin, macijin kuwa ya dawo sanda a hannunsa.

  5. Iliya ya ɗauki yaron ya sauko da shi daga ɗakin sama zuwa cikin gida. Ya ba da shi ga mahaifiyarsa, ya ce, “Duba, ɗanki yana da rai!”

  6. Sai ta ce wa uwargijiyarta, “Da dai shugabana zai ga annabin da yake Samariya, da annabin zai warkar da shi daga kuturtarsa.”

  7. Sai Na’aman ya je wurin maigidansa ya faɗa masa abin da yarinyan nan daga Isra’ila ta faɗa.

  8. Sarkin Aram ya ce, “Ko ta ƙaƙa, ka tafi, zan aika da wasiƙa ga sarkin Isra’ila.” Sai Na’aman ya tashi, ɗauke da talenti goma na azurfa, shekel dubu shida na zinariya, da tufafi kashi goma.

  9. Wasiƙar da ya kai wa sarkin Isra’ila ta ce, “Da wannan wasiƙa ina aika Na’aman gare ka don ka warkar da kuturtarsa.”

  10. Da sarkin Isra’ila ya karanta wasiƙar, sai ya yayyage tufafinsa, ya ce, “Ni Allah ne? Zan iya ɗauke rai ko in mai da shi? Me ya sa wannan mutum ya turo mini wannan mutum in warkar da kuturtarsa? Dubi fa yadda yake nemana da faɗa!”

  11. Da Elisha mutumin Allah ya ji cewa sarkin Isra’ila ya yayyage tufafinsa, sai ya aika masa da wannan saƙo, “Don me za ka yayyage tufafinka? Ka sa mutumin yă zo wurina, zai kuwa san cewa akwai annabi a Isra’ila.”