Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prophets: Frequently in their actions, &c were made signs to the people

67 ayoyi · 128 fannoni

Ayoyi game da Frequently in their actions, &c were made signs to the people

Tace bisa littafi
  1. a wannan lokaci Ubangiji ya yi magana ta wurin Ishaya ɗan Amoz. Ya ce masa, “Tuɓe tsummokin da kake saye da su, da kuma takalman da ka sa a ƙafafu.” Ya kuwa yi haka, yana yawo tsirara kuma ba takalma a ƙafa.

  2. Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kamar dai yadda bawana Ishaya ya yi ta yawo tsirara kuma ba takalmi a ƙafa shekara uku, a matsayin alama da shaida a kan Masar da Kush,

  3. haka sarkin Assuriya zai kwashe kamammun Masarawa da Kushawa tsirara kuma ba takalma a ƙafa, yaro da babba, asirinsu a tsiraice, don a kunyata Masar.

  4. Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Tafi ka sayo tulu a wurin mai ginin tukwane. Ka ɗauki waɗansu dattawan jama’a da kuma na firistoci

  5. “Sa’an nan ka fasa tulun yayinda waɗanda suka tafi tare da kai suna duba,

  6. ka kuma ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa zan farfasa wannan al’umma da wannan birni kamar yadda aka farfasa wannan tulu mai ginin tukwane ba kuwa zai gyaru ba. Za a binne matattu a Tofet har sai ba sauran wuri.

  7. Ga abin da Ubangiji ya ce mini, “Ka yi karkiyar itace da maɗaurai ka ɗaura a wuyanka.

  8. Sa’an nan ka aika da saƙo zuwa wurin sarakunan Edom, Mowab, Ammon, Taya da Sidon ta bakin jakadu waɗanda suka zo Urushalima wurin Zedekiya sarkin Yahuda.

  9. “Yayinda Yahudawa suna kallo, ka ɗauki waɗansu manyan duwatsu tare da kai ka kuma binne su cikin yumɓu a tubalin dakalin ƙofar shiga fadar Fir’auna a Tafanes.

  10. Sa’ad da ka gama karanta wannan littafi, sai ka ɗaura wa littafin dutse, sa’an nan ka jefar da shi tsakiyar Kogin Yuferites.

  11. “Yanzu, ɗan mutum, ka ɗauki tubalin yumɓu, ka ajiye shi a gabanka ka kuma zāna birnin Urushalima a kansa.

  12. Sa’an nan ka yi mata ƙawanya. Ka kafa mata katangar ƙawanya, ka gina katangar da ɗan tudu ka kewaye ta da dundurusai.

  13. Sa’an nan ka ɗauki kwanon ƙarfe, ka shirya shi kamar katangar ƙarfe tsakaninka da birnin ka kuma zuba mata ido. Za tă kasance a ƙarƙashin ƙawanya, kai kuwa za ka yi mata ƙawanya. Wannan zai zama alama ga gidan Isra’ila.

  14. “Sa’an nan ka kwanta a hagunka ka kuma sa zunubin gidan Isra’ila a kanka. Za ka ɗauki zunubinsu na waɗansu kwanakin da kake kwance a gefenka.

  15. Na ɗora maka kwanaki bisa ga shekarun zunubinsu. Saboda haka cikin kwana 390 za ka ɗauki zunubin gidan Isra’ila.

  16. “Bayan ka gama haka, ka sāke kwantawa, a wannan lokaci a gefen damarka, ka kuma ɗauki zunubin gidan Yahuda. Na ɗora maka kwanaki 40, kwana guda a madadin shekara guda.

  17. Ka juya fuskarka wajen ƙawanyar Urushalima da hannunka a buɗe ka yi annabci a kanta.

  18. Zan ɗaura ka da igiyoyi don kada ka juya daga wannan gefe zuwa wani gefe sai ka gama kwanakin ƙawanyarka.

  19. “Ka ɗauki alkama da sha’ir, wake da acca, gero da maiwa; ka sa su a tulun ajiya ka kuma yi amfani da su don yin burodi wa kanka. Za ka ci shi a kwanaki 390 da za ka kwanta a gefenka.

  20. Ka auna shekel ashirin na abinci don kowace rana ka kuma ci shi a ƙayyadadden lokaci.

  21. Haka ma ka auna kashi ɗaya bisa shida na garwan ruwa ka sha shi a ƙayyadadden lokaci.

  22. Ka ci abinci yadda za ka ci ƙosai sha’ir, ka gasa shi a gaban mutane, ka yi amfani da najasar mutane kamar itacen wuta.”

  23. Ubangiji ya ce, “Ta haka mutanen Isra’ila za su ci ƙazantaccen abinci a cikin al’ummai inda zan kore su in kai.”

  24. “Yanzu, ɗan mutum, ka ɗauki takobi mai kaifi ka kuma yi amfani da shi kamar rezan mai aski don askin kanka da gemunka. Sa’an nan ka ɗauki ma’auni ka kuma raba gashin.

  25. Sa’ad da kwanakin ƙawanyarka sun ƙare, sai ka ƙone kashi ɗaya bisa uku na gashin da wuta a cikin birnin. Ka ɗauki kashi ɗaya bisa uku ka yayyanka shi da takobi kewaye da birnin. Ka kuma watsar da kashi ɗaya bisa uku a iska. Gama zan fafare su da takobin da aka zāre.