Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prophets: Felt deeply on account of the calamities which they predicted

10 ayoyi · 128 fannoni

Ayoyi game da Felt deeply on account of the calamities which they predicted

  1. Saboda haka na yi kuka, yadda Yazer take kuka, saboda inabin Sibma. Ya Heshbon, ya Eleyale, na cika ku da hawaye! Sowa ta murna a kanku saboda ’ya’yan itatuwanku da suka nuna da kuma girbinku sun ɓace.

  2. An ɗauke farin ciki da murna daga gonakin itatuwa masu ’ya’ya; babu wanda yake rerawa ko yake sowa a cikin gonakin inabi; babu wanda yake matsin ruwan inabi a wuraren matsi, gama na kawo ƙarshen yin sowa.

  3. Zuciyata tana makoki saboda Mowab kamar garaya, na yi baƙin ciki saboda Kir Hareset.

  4. Da ma kaina maɓulɓulan ruwa ne idanuna kuma maɓulɓulan hawaye! Da sai in yi kuka dare da rana saboda mutanena da aka kashe.

  5. Da ma a hamada ina da wurin da matafiye za su sauka, don in bar mutanena in tafi in bar su; gama dukansu mazinata ne, taron mutane marasa aminci.

  6. “Sun tanƙwasa harshensu kamar baka, don su harba ƙarya; ba da gaskiya ba ne suke nasara a cikin ƙasar. Sukan tashi daga wannan zunubi zuwa wancan; ba su san ni ba,” in ji Ubangiji.

  7. “Ka yi hankali da abokanka; kada ka amince da ’yan’uwanka. Gama kowane ɗan’uwa munafuki ne, kowane aboki kuma mai kushe ne.

  8. Aboki kan ruɗi aboki, ba mai faɗar gaskiya. Sun koya wa harshensu faɗar ƙarya; sun gajiyar da kansu da yin zunubi.

  9. Kai kana zama a tsakiyar ruɗu; cikin ruɗunsu sun ƙi su san ni,” in ji Ubangiji.

  10. Saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Ga shi zan tace in kuma gwada su, gama me kuwa zan yi saboda zunubin mutanena?