Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prophets: David
Ayoyi game da David
Kullum nakan sa Ubangiji a gabana. Gama yana a hannun damana, ba zan jijjigu ba.
Saboda haka zuciyata tana murna harshena kuma yana farin ciki; jikina kuma zai zauna lafiya,
domin ba za ka yashe ni a kabari ba, ba kuwa za ka bar Mai Tsarkinka yă ruɓa ba.
Ka sanar da ni hanyar rai; za ka cika ni da farin ciki a gabanka, da madawwamin jin daɗi a hannun damarka.
Dawuda ya yi faɗi game da shi cewa, “ ‘Kullum ina ganin Ubangiji a gabana. Gama yana a hannuna na dama, ba zan jijjigu ba.
Amma shi annabi ne ya kuma san abin da Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa zai ɗora ɗaya daga cikin zuriyarsa a kan gadon sarautarsa.