Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prophets

655 ayoyi · 128 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Mahaifinsa Zakariya ya cika da Ruhu Mai Tsarki sai ya yi annabci ya ce,

  2. (yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki),

  3. To, akwai wani mutum a Urushalima mai suna Siman, shi mai adalci da kuma mai ibada. Yana jiran fansar Isra’ila, Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi.

  4. An bayyana masa ta wurin Ruhu Mai Tsarki cewa ba zai mutu ba sai ya ga Kiristi na Ubangiji.

  5. Da Ruhu ya iza shi, sai ya shiga cikin filin haikali. Sa’ad da iyayen suka kawo jaririn nan Yesu don su yi masa abin da al’adar Doka ta bukaci,

  6. Akwai wata annabiya ma, mai suna Anna, diyar Fanuwel, na kabilar Asher. Ta tsufa kutuf; ta yi zama da mijinta shekaru bakwai bayan sun yi aure,

  7. A lokacin ne Annas da Kayifas suke manyan firistoci. Sai maganar Allah ta zo wa Yohanna, ɗan Zakariya a hamada.

  8. Aka kuwa ba shi naɗaɗɗen littafin annabi Ishaya. Da ya buɗe, sai ya sami wurin da aka rubuta,

  9. Ya ci gaba, da ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, babu annabin da ake yarda da shi a garinsa.

  10. Ina tabbatar muku a zamanin Iliya, akwai gwauraye da yawa a Isra’ila, sa’ad da aka rufe sararin sama har shekara uku da rabi, aka kuma yi yunwa mai tsanani ko’ina a ƙasar.

  11. Duk da haka, ba a aiki Iliya ga ko ɗaya a cikinsu ba. Sai dai zuwa ga wata gwauruwa da take a Zarefat, a yankin Sidon.

  12. Akwai kuma mutane da yawa a Isra’ila masu kuturta a zamanin annabi Elisha, amma ba ko ɗayansu da aka tsarkake sai Na’aman mutumin Suriyan nan kaɗai.”

  13. Saboda haka, alhakin jinin dukan annabawa da aka kashe, tun farkon duniya, yana kan wannan zamani,

  14. “Urushalima, ayya Urushalima, ke da kika kashe annabawa, kuma kika jefa wa waɗanda aka aika gare ki da duwatsu. Sau da yawa na yi kewan in tattara ’ya’yanki wuri ɗaya, kamar yadda kaza takan tattara ’ya’yanta cikin fikafikanta, amma ba ki yarda ba!

  15. Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da na gaya muku tun ina tare da ku cewa, dole a cika kome da aka rubuta game da ni, a cikin Dokar Musa, da Annabawa, da kuma Zabura.”

  16. Akwai wani mutumin da aka aiko daga Allah; mai suna Yohanna.

  17. Filibus ya sami Natanayel ya kuma gaya masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta game da shi a cikin Doka, kuma wanda annabawa suka rubuta a kansa, Yesu Banazare, ɗan Yusuf.”

  18. (To, Yesu kansa ya taɓa faɗa cewa annabi ba shi da daraja a ƙasarsa.)

  19. Ba zato ba tsammani sai aka ji motsi kamar ta babbar iska tana hurowa daga sama ta kuma cika dukan gidan da suke zaune.

  20. Suka ga wani abin da ya yi kama da harsunan wuta, suka rarrabu suna kuma sassauka a kan kowannensu.

  21. Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki suka kuma fara magana da waɗansu harsuna yadda Ruhu ya sa suka iya.

  22. A’a, ai, abin da aka yi magana ta bakin annabi Yowel ke nan cewa,

  23. Dawuda ya yi faɗi game da shi cewa, “ ‘Kullum ina ganin Ubangiji a gabana. Gama yana a hannuna na dama, ba zan jijjigu ba.

  24. Amma shi annabi ne ya kuma san abin da Allah ya yi masa alkawari da rantsuwa cewa zai ɗora ɗaya daga cikin zuriyarsa a kan gadon sarautarsa.

  25. Amma ta haka ne Allah ya cika abin da ya rigyafaɗi ta bakin dukan annabawa cewa, Kiristinsa zai sha wahala.